Jerin ma'aikatun gwamnatin Najeriya 3 da ke daukar aiki a halin yanzu
- Domin karin hannaye a gudanar da ayyukansu, wasu hukumomin gwamnati na neman karin ma'aikata
- Kowace hukuma ta bayyana abubuwan da ta ke bukat, da kuma lokutan da za a rufa cike fom
- Hakazalika, bayanai da ake bukata wajen cike ayyukan sun bayyana dalla-dalla ga masu sha'awar shiga
Ga 'yan Najeriya masu neman aikin yi, a halin yanzu hukumomin gwamnati uku ne ke daukar ma'aikata yayin da suke neman samun karin hannaye don gudanar da ayyukansu.
Legit.ng ta tattaro muku jerin ma'aikatu da hukumomin gwamnatin da suke daukar aiki a halin yanzu.
Ga su kamar haka:
1. Sojin Najeriya
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rundunar Sojin Najeriya ta fara atisayen daukar sabbin ma'aikata 82 a tsarin daukar ma'aikata na yau da kullum.
Duk cike-cike da aka tura za a tantance su ta yanar gizo, daga nan kuma za a kira wadanda suka yi nasara domin tantance su a zahiri a cibiyar kaukar ma'aikatan tsrao ta Kaduna wacce aka fi sani Ribadu Cantonment, da ke Kaduna.
Fom din neman aikin kyauta ne kuma yana nan a kafar yanar gizo ta soji wato https://recruitment.army.mil.ng.
Hakazalika, za a rufe fom din a ranar Juma'a, 26 ga Nuwamba.
2. Hukumar Kula da Shaidar Mazauna Jihar Kaduna
Haka kuma hukumar kula da shaidar mazauna jihar Kaduna yanzu haka tana daukar ma'aikata.
Hukumar tana kira ga wadanda suka cancanta da su nemi wadannan mukamai kamar haka:
- Department Head - Operations
- Unit Head – Admin Unit
- Head – Finance
- Unit Head – Inter-Agency Support
- Monitoring And Evaluation Officer
- Customer Service Officer
- Information And Data Management Officer
- Unit Head – Information And Data Management
- Unit Head – Customer Service
- Unit Head – Monitoring And Evaluation
- Admin Officer
- Finance Officer
- Inter-Agency Officer
Bi wannan likau din don neman daya daga cikin ayyukan sama. Za a rufe cike fom a ranar Lahadi, 31 ga Oktoba.
3. Shirin gwamnatin Kaduna na 'Video Stack Hackathon'
Cibiyar KADA Hive Innovation and Technology hub, wani shiri ne na gwamnatin jihar Kaduna, da ke neman mai masanin yaren na'ura kuma kwararre don habaka dandalin sadarwa na bidiyo.
Gwamnatin Nasir El-Rufai na kira ga kwararru da su samar da wani dandamali don watsa shirye-shiryen bidiyo na abubuwan cikin gida a zaman wani bangare na tsare-tsaren dabarun sa na kirkiro sabbin abubuwa a jihar Kaduna.
Baya ga ba da kwangilar kirkirar dandalin bidiyo, wanda ya ci nasara/suka ci nasarar zai/za su sami kyautar kudi N250,000.00.
Masu sha'awa za su iya shiga a matsayin kungiya ko mutum daya. Idan kuna da sha'awar, zaku iya tura bukatar hakan ta wannan likau da gwamnati ta bayar:
https://kadahivehub.com/video-stack-hackathon/?fbclid=IwAR29hXniS3EoZ6RUQ4n93vTCyxeAy-Ab_wkTFoOTagH4Ck6MBHUhAPg4zoQ
Za a rufe dauka a ranar Lahadi Oktoba, 17.
Daukar aikin sojin sama: Abubuwa 14 da wadanda aka zaba suke bukatar tanada nan kusa
A wani labarin, Rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF) ta fitar da sunayen wadanda suka yi nasara don samun horo na Basic Military Training Course (BMTC 42/2021) daga cikin wanda suka nuna sha'awar shiga aikin sojin sama.
AVM Mahmud Nda Madi ne ya rattaba hannu kan jerin sunayen da aka fitar a madadin babban hafsan sojin sama sannan aka yada a shafin Facebook na NAF a ranar Asabar 16 ga watan Oktoba.
An nemi wanda suka yi nasarar da su zo domin fara karbar horo a Cibiyar Horar da Sojojin Najeriya da ke Kaduna ranar Asabar, 30 ga Oktoba, 2021.
Asali: Legit.ng