Yadda 'Ruwa mai tsarki' ya raba Mata da Miji da suka shekara 10 suna gina soyayya
- Wani magidanci ya garzaya babbar kotun jihar Legas yana neman alkali ya raba shi da matarsa da suka shekara 10 tare da juna
- Mutumin ya shaida wa alkalin cewa ya gudu daga gidan aurensa saboda yana zargin matar da shiga bokanci, bayan yaga wata kwalbar ruwa a gidan
- Matar dai ta faɗa wa alkalin cewa dama can mijinta ya taba shaida mata cewa babu sauran zaman lafiya a tsakaninsu
Lagos - Wasu ma'aurata sun garzaya gaban babban kotun jihar Legas, suna neman alkali ya raba aurensu da ya kwashe shekara 10.
Guardian ta ruwaito cewa hakan ya faru ne saboda wata kwalba ɗauke da, 'Ruwa mai tsarki, wato na addu'a' da matar ta kawo cikin gidan aurenta ba tare da sanin mijin ba.
Magidancin, Olaniyi Oluwaseun Oladepo, ya roƙi alkalin kotun, mai shari'a Christopher Balogun, ya raba shi da matarsa, Adeyinka.
Yadda Matar Aure Ta Zama Mai Aikin Goge-goge Don Tura Mijinta Makaranta A Kasar Waje, Bidiyon Ya Yadu
Oladepo ya yi ikirarin cewa matar ta nemi faɗa da shi ne, shiyasa ta kawo wannan kwalban ruwan cikin gidansa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Meyasa mijin yake neman a raba auren?
Mijin ya shaidawa alƙalin kotun cewa shifa guduwa ya yi daga gidan aurensa saboda yana zargin matar da fara tsubbace-tsubbace.
A jawabinsa yace:
"Inajin kamar tana mun barazana ne, saboda haka na ɗauki matakin tserewa daga gidan, domin naga wani ruwa da bansan da zuwansa ba."
Shin matar ta amsa zargin da mijin ke mata?
Da take martani kan zargin, Matar Oladepo ta bayyana wa kotu cewa ta auri maigidanta ne tun a ranar 15 ga watan Oktoba, 2011.
"Muna da 'ya'ya guda biyu, daya yakai shekara 5, yayin da ɗan uwansa ya kai shekara 7 a duniya."
Matar ta bayyana cewa tun a shekarar 2015 mijinta ya tabbatar mata da cewa babu sauran jituwa a tsakaninsu.
Daga ina kwalbar ruwan ta fito?
A jawabin matar tace:
"Mahaifiyata ce ta zo da kwalbar ruwan addu'a daga Coci, kuma ni amsar ruwan kawai na yi amma ban yi amfani da shi ba."
"Na yi tafiya zuwa wurin aiki, bayan nadawo sai na tarad da mijina ya bar gidan, ya ma gudu daga gidan auren mu."
Daga ƙarshe dai, Alkalin kotun ya sanar da ɗage sauraron ƙarar har zuwa wani lokaci nan gaba.
A wani labarin kuma mun tattaro muku Jerin Fitattun Jaruman Kannywood 5 da suka taba fitowa takarar siyasa a Najeriya da mukaman da suka nema
A cikin masana'antar fina-finan Hausa wacce aka fi sani da Kannywood, akwai wasu jarumai da suka taba kokarin nuna bajintarsu a fagen siyasa.
Waɗannan jarumai sun fito takara a matakai daban-daban na yankunansu, kuma a dokar ƙasa kowa na da damar fitowa takara matukar ya cike ƙa'idojin hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC.
Asali: Legit.ng