'Yan bindiga sun sako sarkin Bunguda na Zamfara bayan shafe kwanaki a hannunsu
- A jihar Zamfara, an sako wani sarkin gargajiya da 'yan bindiga suka yi awon gaba da shi
- An sace sarkin ne tun ranar 14 ga watan satumba, kwanaki sama da 30 da suka gabata kenan
- Majiya daga gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da sakin sarkin, tare da mika godiya ga hukumomi
Zamfara - Kwanaki sama da 30 bayan sace shi, Sarkin Bungudu ta jihar Zamfara, Alhaji Hassan Attahiru, ya sake samun 'yanci daga hannun 'yan bindiga.
A baya mun ruwaito muku cewa, an yi garkuwa da sarkin ne yayin da wasu 'yan bindiga suka dira wa ayarin motocin sa a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar 14 ga watan Satumba.
Rahoton Daily Trust ya ce, wata majiyar tsaro ta ce an saki sarkin ne da yammacin ranar Asabar a jihar Kaduna.
Gazali Shehu Ahmad, wani mai ba da shawara na musamman ga gwamna Bello Matawalle kan dabaru, ya tabbatar da sakin sarkin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A wani rubutu da ya yi a Facebook, ya rubuta cewa:
"A madadin iyalan Sarki da masarautar Bungudu muna mika sakon godiya zuwa ga al'umma domin addu'a da taimako ta hanyoyi daban daban da suka bayar tun faruwar wannan al'amari har zuwa yau.
"Muna mika godiya zuwa ga gwamnatin jihar Kaduna bisa kokarin da sukayi tayi tun ranar da akayi garkuwa da Sarki har zuwa lokacin daya samu dawowa.
"Muna mika godiya ta musamman zuwa ga gwamnatin jihar Zamfara karkashin shugabancin Hon. Dr. Bello Mohammed (Matawallen Maradun) bisa gagarumin kokarin da tayi domin ganin Sarki yasamu dawowa gida lafiya.
"Muna jinjina zuwa ga hukumar yan' sanda da kungiyar Miyetti Allah bisa kokarin da sukayi na ganin Sarki yadawo gida lafiya.
"Muna rokon al'umma dasu cigaba da yima Sarki addu'a zuwa wasu yan kwanaki nan gaba da zai nemi lafiya da kuma samun natsuwa kafin yadawo ya gana da al'umma.
A baya rahotanni sun bayyana cewa, an sake sarkin Bungudu lokacin da yake tafiya tare da ayarin motocinsa a hanyar Kaduna.
Wannan ba shine karon farko da aka fara sace mai sarauta a yankin Arewa maso yamma ba, an samu da dama a yankin.
Manyan sarakunan arewa guda 6 da ‘yan bindiga suka sace
Kun ji cewa, Matsalar sace-sacen mutane don karbar kudin fansa na kara kamari a Najeriya, inda ba a bar sarakuna ba ma musamman a yankin arewa.
Zuwa yanzu an sace sarakuna da dama daga yankin arewa wanda na baya-ayan nan da aka yi shine na Basaraken Bungudu a hanyarsa ta zuwa Abuja daga Kaduna.
Ga jerin wasu daga cikin sarakunan da mahara suka sace amma dai sun sako su illa na Bungudu da ke hannu a halin yanzu.
Asali: Legit.ng