Da duminsa: Hukumar EFCC ta yiwa tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso tambayoyi

Da duminsa: Hukumar EFCC ta yiwa tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso tambayoyi

  • Bayan makonni ana gayyatarsa, Rabiu Kwankwaso ya leka ofishin hukumar EFCC
  • Majiya a EFCC ta bayyana cewa tsohon gwamnan ya sha tambayoyi
  • EFCC na binciken Sanata Kwankwaso kan zargin almundahana

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso , ya mika kansa ga hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC.

Premium Times ta ruwaito cewa Kwankwaso ya kai kansa hedkwatar hukumar dake unguwar Jabi, birnin tarayya Abuja.

Majiyoyi a EFCC sun bayyana cewa Kwankwaso ya isa ofishin misalin karfe 12 na ranar Asabar.

Daya daga cikin majiyoyin ta bayyana cewa an dade ana gayyatarsa ana baya uwa.

A cewar majiyar:

"Yazo wannan karon bayan an dade ana gayyatarsa ba ya zuwa,"

Kara karanta wannan

Sabbin bayanai kan shirin sauya shekar tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Kwankwaso, zuwa APC

Da duminsa: Hukumar EFCC ta turke tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso
Da duminsa: Hukumar EFCC ta turke tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: EFCC
Asali: UGC

Dalilin gayyatar Kwankwaso?

Sanadin binciken shine wani takardan korafi da kungiyar 'yan fansho da ma'aikatan jihar Kano suka shigar a 2015, inda suka yi ikirarin Kwankwaso ya sabawa dokar Garatuti ta 2007 yayin rike kudin fansho da ya kai Naira biliyan 10 daga 2011 zuwa 2015.

Kwankwaso ya yi gwamna a Kano tsakanin 2011 zuwa 2015. A baya, ya rike mukamin daga 1999 zuwa 2003.

A cewar masu korafin, Kwankwaso ya bada umurnin a yi amfani da kudin fanshon wurin gina gidaje da ya kamata mafi yawancin yan fanshon su amfana da su.

An cimma yarjejeniya tsakanin hukumar fansho ta Kano, a matsayin masu saka jari, yayin da gwamnatin Kano da Hukumar Gidaje na Kano za su yi aikin a kasafi na 60:40.

Kara karanta wannan

Sakin Nnamdi Kanu zai kawo ƙarshen rashin tsaro a kudu maso gabas, Sanata Ubah

Sai dai bayan bada kwangilan gina gidaje 1,579 a 'biranen Kwankwasiya, Amana da Bandarawa' masu karar sun yi ikirarin Kwakwaso ya saba wasu alkawuran da aka yi ya rika bawa wasu na kusa da shi gidaje.

Sun yi zargin lamarin ya faru ne a Mayun 2015, watan da Kwankwaso ya bar ofis a matsayin gwamna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng