Allah ya yi wa matar Marigayi Sheikh Abubakar Gumi rasuwa
- Allah ya yi wa Hajiya Aminatu Bintu, matar Marigayi Sheikh Abubakar Gumi rasuwa
- Marigayiyar ta rasu ne a safiyar ranar Asabar, 16 ga watan Oktoba
- Za a yi jana’izarta da misalin karfe 4.30 pm bayan Sallar La'asar a gidan Sheikh Ahmed Gumi
Matar Marigayi Sheikh Abubakar Gumi, Hajiya Aminatu Bintu ta rasu a safiyar yau Asabar, 16 ga watan Oktoba.
Labarin mutuwar tata na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shahararren malamin nan na addinin Musulunci, Sheikha Ahmed Gumi ya fitar a shafinsa na Facebook.
Marigayiyar ta kasance mahaifioya ga Birgediya Janar Abdulkadir Gumi. Kuma za a yi jana’izarta da karfe 4:30 na yamma a gidan Sheikh Gumi.
Ya rubuta a shafin nasa:
“Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun.
“Allah yayiwa Hajiya Aminatu Bintu rasuwa. Matar Marigayi Sheikh Abubakar Gummi, dazu da safe. Mahaifiyar su Brigadier General Abdulkadir Gumi.
“Za ayi Janazarta anjima a gidan Sheikh Abubakar Gumi da karfe 4.30 pm bayan Sallar La'asar.
“Allah ya jikanta ya gafarta mata da sauran al'umma baki daya amin.”
Rai bakon duniya: Babban alkalin kotun daukaka kara na Kano ya kwanta dama
A wani labarin, mun kawo a baya cewa Babban alkalin kotun daukaka kara na jihar Kano, mai shari'a Hussein Mukhtar, ya rasu yayin da yake shekaru 67.
Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, majiyoyi daga iyalansa sun ce ya rasu a sa'o'in farko na ranar Asabar a Abuja bayan gajeriyar rashin lafiya.
Marigayin alkalin ya fara aikinsa da ma'aikatar shari'a na jihar Bauchi daga watan Yunin 1976 zuwa watan Oktoban 1992.
Asali: Legit.ng