Rai bakon duniya: Babban alkalin kotun daukaka kara na Kano ya kwanta dama

Rai bakon duniya: Babban alkalin kotun daukaka kara na Kano ya kwanta dama

  • Allah ya yi wa babban alkalin kotun jihar Kano, mai shari'a Hussein Mukhtar, rasuwa
  • Majiyoyi daga iyalan mamacin sun tabbatar da cewa ya rasu a sa'o'in farko na ranar Asabar
  • Kafin ya zama babban alkalin, ya yi aiki a wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a matsayin magatakarda

Kano - Babban alkalin kotun daukaka kara na jihar Kano, mai shari'a Hussein Mukhtar, ya rasu yayin da yake shekaru 67.

Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, majiyoyi daga iyalansa sun ce ya rasu a sa'o'in farko na ranar Asabar a Abuja bayan gajeriyar rashin lafiya.

Rai bakon duniya: Babban alkalin kotun daukaka kara na Kano ya kwanta dama
Rai bakon duniya: Babban alkalin kotun daukaka kara na Kano ya kwanta dama. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Marigayin alkalin ya fara aikinsa da ma'aikatar shari'a na jihar Bauchi daga watan Yunin 1976 zuwa watan Oktoban 1992.

Kara karanta wannan

Yarimomi 45 sun shiga jerin masu neman mulkin Sarkin Sudan na Kontagora

An kira shi zuwa makarantar horar da lauyoyi masu zaman kansu a 1981 inda ya zama lauya mai zaman kansa kuma lauyan kotun koli a Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya taba kasancewa alkalin kotun majistare, sakataren hukumar shari'a ta jihar Bauchi kuma magatakarda babbar kotun tarayya ta Abuja.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, tsohon alkalin ya kasance ma'aikacin kotun daukaka kara tun daga 2006.

2023: APC ta magantu kan rade-radin za ta bai wa Jonathan tikitin takara shugabancin kasa

A wani labari na daban, jam’iyyar APC ta ce ba ta tabbatar wa da tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan tabbacin tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023 ba, kamar yadda ake ta yadawa.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, sakataren CECPC, John Akpanudoedehe ya bayyana hakan a wata takarda a Abuja ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

An saki bidiyo yayin da kwamandan IPOB/ESN Shakiti-Bobo ya ambaci sunan mai daukar nauyin kungiyoyin

Akpanudoedehe ya yi karin haske ne a kan sauya fahimtar sa da aka yi na rangwamen da NEC ta bai wa sababbin mambobin jam’iyya da masu sauya sheka a wani taron su da suka yi a ranar 8 ga watan Disamban 2020.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel