Da Duminsa: Gwamnatin tarayya ta bada hutun Maulidi a Najeriya

Da Duminsa: Gwamnatin tarayya ta bada hutun Maulidi a Najeriya

  • Sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida, Shuaib Belgore ya sanar da ranar Talata ta zama hutu a Najeriya a ranar Juma’a
  • Ranar Talata, 19 ga watan Oktoban 2021 za ta kasance hutu saboda murnar shagalin haihuwar fiyeyyen halitta, Annabi Muhammadu SAW
  • A takardar da Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ya bayar, ya ce ya na taya daukacin al’ummar musulmin Najeriya murna

Abuja - Gwamnatin tarayya ta sanar da ranar Talata, 19 ga watan Oktoba ta zama hutuna wannan shekarar saboda shagalin murnar haihuwar Annabi Muhammadu SAW.

Kamar yadda ma'aikatar harkokin cikin gida ta fitar a shafinta na Facebook, sakataren ma’aikatar cikin gida, Shuaib Belgore ne ya bayyana hakan ta wata takarda ta ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

Jerin Fitattun Jaruman Kannywood 5 da suka taba fitowa takarar siyasa da kujerun da suka nema

Da Duminsa: Gwamnatin tarayya ta bada hutun Maulidi a Najeriya
Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola. Hoto: Ma'aikatar Cikin Gida
Asali: Facebook

Ministan harkokin cikin gida ya na taya musulmai murna

Kamar yadda takardar ta zo, ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ya na taya daukacin al’ummar musulmai murnar ganin wannan babbar rana ta wannan shekarar.

Aregbesola ya shawarci ‘yan Najeriya da su kasance masu hakuri, juriya da kaunar juna wadanda duk dabi’un annabi Muhammadu SAW ne, inda ya kara da cewa su kasance ma su yi wa kasa addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Aregbesola ya bayyana a takardar cewa:

“Ogbeni Aregbesola ya na rokon dukan ‘yan Najeriya musamman musulmai su guje daga duk harkokin tayar da tarzoma da duk wasu dabi’u marasa kyau. Mu taru mu nuna cewa mu shugabannin nahiyar Afirka ne masu nagarta.”

Ya yi kira akan dakatar da duk wasu abubuwan da za su janyo rabuwar kawuna a fadin kasa, inda ministan ya bukaci ‘yan Najeriya, musamman matasa su rungumi yin aiki tukuru, jajircewa akan gaskiya da zaman lafiya duk da bambance-bambancen addinai.

Kara karanta wannan

Ba zan iya zama da ita ba saboda bata yin wanka kullum, Miji ya nemi a raba aurensa da masoyiyar matarsa

Sannan su ba gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari hadin kai don tabbatar da ci gaban kasa baki daya.

Abin da yasa har yanzu Nigeria bata zama ƙasaitacciyar ƙasa ba, Ministan Buhari

A wani rahoton, ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, ya ce har yanzu Nigeria bata cimma babban matakin da ake sa ran ta kai ba a lokacin samun 'yanci saboda an yi watsi da irin halayen mazajen jiya da suka kafa kasar.

Ya yi wannan jawabi ne a babban birnin tarayya Abuja wurin wani taro da kungiyar 'Yan Kabilar Igbo ta shirya don karrama Rear Admiral Godwin Kanu Ndubuisi (mai ritaya), Daily Trust ta ruwaito.

Onu ya ce ya zama dole 'yan Nigeria su zama masu gaskiya, aiki tukuru da riko da halaye na gari idan suna son ganin kasar ta zama tauraro tsakanin sauran kasashe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164