Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya gana da Fasto Tunde Bakare a fadar shugaban kasa
- Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya sa labule tare da babban Faston nan na Najeriya, Tunde Bakare
- Buhari ya tarbi Bakare ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja, a ranar Juma'a, 15 ga watan Oktoba
- Kakakin shugaban kasar, Femi Adesina ne ya sanar da batun ganawar tasu, sai dai bai bayar da cikakken bayani kan abun da za su tattauna ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton
Fadar shugaban kasa, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Shugaban cocin CGCG, Fasto Tunde Bakare, a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Juma’a, 15 ga watan Oktoba.
Mataimakin shugaban kasa na musamman a kan harkokin labarai, Femi Adesina ne ya bayyana hakan inda ya yada hotunan ganawar a shafinsa na Facebook.
Adesina ya rubuta a saman hotunan:
“Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Fasto Tunde Bakare a fadar shugaban kasa a ranar 15 ga watan Oktoba 2021.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sai dai hadimin shugaban kasar, ya ki bayyana abun da ganawar tasu ta kunsa.
Ya kamata Buhari ya yage tsarin mulkin 1999, saboda kakaba mana shi aka yi, Bakare
A baya-bayan nan ne muka ji cewa Fasto Tunde Bakare, ya roki Shugaba Muhammadu Buhari da ya jagoranci canjin kundin tsarin mulkin 1999, Daily Trust ta ruwaito.
Ya ce kundin tsarin mulkin na yanzu shi ne jigon matsalar da Najeriya ke fuskantar, yana mai bayyana shi a matsayin “daukakiyyar takardar shaidar mutuwa.”
Da yake magana a gidan rediyo a jihar Legas, Bakare ya kalubalanci Buhari da ya daina mika wa Majalisar Dokoki ta kasa komai.
Ya ce tsarin mulkin 1999 wanda aka fara da, "Mu Jama'a" sojoji ne suka kakabawa 'yan Najeriya shi.
Bakare ya sake nanata cewa sake fasalin Najeriya da sauya kundin tsarin mulki ya fi muhimmanci fiye da tattauna batun canjin mulki.
Asali: Legit.ng