Shehu Sani ya bayyana wani sirri mai ban dariya game da matarsa da diyarsa
- Shehu Sani ya bayyana cewa a kodayaushe matarsa na zuba ido don ganin abun da wayarsa ta kunsa
- A cewar tsohon sanatan na Kaduna, a kullun diyarsa kan dakile kokarin matarsa na son damkar wayar
- A halin da ake ciki, ‘yan Najeriya da dama a Facebook sun yi martani ga lamarin, sun bukaci Sani da ya bari matarsa ta duba wayar
Kaduna – Tsohon sanatan Kaduna, Shehu Sani ya bayyana cewa a kodayaushe diyarsa kan dakile kokarin matarsa na ganin ta damki wayarsa.
Sanatan mara shayin magana wanda ya sauya sheka zuwa babbar jam’iyyar adawa ta People Democratic Party (PDP) a kwanan nan ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook.
Ya rubuta:
“A duk lokacin da na bai wa diyata wayata domin ta buga wasanni da shi, sai na lura cewa mahaifiyaryta ta kan so kiranta zuwa kicin; diyar tawa mai wayo sai ta mika mani wayar kafin ta tafi kicin din; toh daga nan sai ka ga mahaifiyar tana bata rai. Ina son diyata.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A halin yanzu, martani sun biyo bayan wallafar mai ban dariya a Facebook.
Babangida Danlawal Gumau a martaninsa ya rubuta:
“Yara mata masu wayo basa zama tushen rigima tsakanin iyayensu don ganin zaman lafiya ya ci gaba da dorewa a cikin iyalin."
Hon Ahmed Tijjani Mustaph ma ya rubuta:
“Yarinya mai wayo, tamkar Uba, tamkar diya, dan’uwana na hango wayonka a tattare da ita. Ina matukar alfahari da ita, Allah Ya raya Mana."
Philip Ibrahim:
“Kwamrad dan Allah ka bari uwargida ta buga wasanni da wayarka itama. Bayan duk kyautar da ta baka na wannan kyakkyawar siya.”
Taiwo Adediran:
“Tana nuna kauna ga iyayen, bata so ta haddasa bala’I, tana son kowa ya kasance cikin farin ciki.”
Magidanci ya tattara kayansa ya bar gida, ya ce matarsa na yawan dukansa, bidiyon ya haddasa cece-kuce
A wani labarin, wani bidiyo na wani dan Najeriya da aka nuno yana korafi bayan 'matarsa farar fata' ta fatattake shi a Burtaniya ya yadu a shafin Twitter tare da martani masu tarin yawa.
A wani rubutu da aka yi a ranar Juma'a, 21 ga Mayu, wani shafin Twitter @Oluomoofderby wanda ya yada bidiyon ya yi masa lakabi da: "Wasu mazan Najeriya na matukar shan wahala a Burtaniya."
A cikin faifan bidiyon, Tunde tare da jakunkunan kayansa a waje da kuma faffadan Talbijin ya yi magana mai daci kan yadda duk da biyan kudin jingina da kuma tsabtace gidan da yake yi, amma matar ta hana sa kwanciyar hankali.
Asali: Legit.ng