Tsoho mai shekaru 60 ya kashe ɗansa mai shekaru 32 saboda saɓani da ya shiga tsakaninsu

Tsoho mai shekaru 60 ya kashe ɗansa mai shekaru 32 saboda saɓani da ya shiga tsakaninsu

  • Wani mahaifi mai shekaru 60 ya halaka dan cikinsa a jihar Enugu
  • Mahaifin ya kashe dansa ne kan ikirarin dan ya yi barazanar zai halaka shi
  • Tuni dai yan sanda sun yi ram da mahaifin kuma sun fara zurfafa bincike

Enugu - Yan sanda a Enugu sun kama wani mutum mai shekaru 60, Ikechukwu, saboda kashe dansa a garin Ogbozinne-Ndiagu Akpugo a karamar hukumar Nkanu West na jihar a ranar Alhamis, 14 ga watan Oktoba.

Mutumin mai 'ya'ya hudu ya kashe dansa ne a ranar Alhamis a kan ikirarin cewa dansa mai shekaru 32 ya yi barazanar zai halaka shi kan wani rashin jituwa da ba a gano ba, The Punch ta ruwaito.

Tsoho mai shekaru 60 ya halaka ɗansa mai shekaru 32 saboda saɓani da ya shiga tsakaninsu
Hedkwatar 'yan sanda na jihar Enugu. Hoto: LIB
Asali: Facebook

A cewar ruwayar jaridar The Punch, Ikechukwu a daren ranar Laraba ya kira shugaban kauyensu kan cewa dansa ya yi barazanar zai kashe shi yayin da suke musayar kalamai.

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan sanda sun yi ram da matasa 3 da ke barazanar sace magidanci idan bai biya N2m ba

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Nan take shugaban kauyensu ya sanar da babban jami'in tsaro wanda shi da tawagarsa suka ziyarci gidan Ikechukwu don yin sulhu.

A cewar shaidan gani da ido, a yayin da jami'in tsaron da tawagarsa suke kokarin yin sulhu tsakanin mahaifin da dansa, Ikechukwu ya yi amfani da digarsa ya yi wa dansa rauni a baya.

Daga bisani dansa ya ce ga garinku da safe. Ya yi kokarin ganin an birne shi amma makwabtansa suka hana shi kuma suka sanar da 'yan sanda.

Abinda 'yan sanda suka ce kan lamarin

Kakakin yan sandan jihar, Daniel Ndukwe ya tabbatar da afkuwar lamarin yana mai cewa an kama mutane uku da ake zargi da hannu.

Ndukwe ya ce:

"An kama mutane uku da ake zargi a kan batun na zargin hadin baki da kisan gilla. Ana bincike a sashin binciken manyan laifuka na CID, jihar Enugu.

Kara karanta wannan

Zamfara: A kalla rayuka 12 sun salwanta, 'yan bindiga sun kone motar 'yan sanda

"Mahaifin marigayin da shugaban tsaro na kauyen suna taimakawa yan sanda a bincikensu."

Mutane su na barazanar halaka ni, Likitan Najeriya da ya buɗe wurin gwajin DNA tare da yin rahusa na kashi 70

A wani labarin daban, wani likita wanda ya bude wurin gwajin kwayoyin halitta na DNA a anguwarsu ya bayyana yadda wasu mutane suke barazanar halaka shi a shafin sa na dandalin sada zumunta sakamakon zargin zai zama kalubale ga aurensu.

Kamar yadda Pulse Nigeria ta ruwaito, likitan mai suna Dr Penking ya bayyana cewa zai bude wurin gwajin DNA din a jihar Legas ne kuma zai samar da rahusar kaso 75 bisa dari a watan Oktoba.

Mutane da dama sun yarda da cewa wannan rahusar za ta bai wa maza da yawa damar tabbatar wa idan su ne iyayen yaran su na hakika, hakan ya kada ruwan cikin jama’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164