'Ku Taimaka Mani': Ɗan Arewa Ya Roki Najeriya bayan Tilasta Masa Shiga Soja a Rasha
- Wani ɗan Najeriya mai suna Abubakar Adamu ya roƙi gwamnatin tarayya ta dawo da shi gida daga kasar Rasha
- Mutumin yana zargin an yaudare shi zuwa Rasha ne bayan ce masa za a ba shi aikin kula da gida a matsayin mai gadi
- Lauyoyinsa sun ce ya je Moscow da bizar yawon buɗe ido amma aka kwace masa takardunsa, aka tilasta masa shiga soja
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Moscow, Russia - Wani ɗan Najeriya mai suna Abubakar Adamu ya koka kan tilasta masa shiga aikin soja a Rasha.
Abubakar Adamu ya roƙi gwamnatin tarayya da ta gaggauta dawo da shi gida daga ƙasar Rasha inda ake ta fama da yaki.

Source: Getty Images
Yadda aka yaudari 'dan Najeriya a Rasha
Ya ce an yaudare shi ne da alkawarin aikin gadi kafin daga bisani aka tilasta masa shiga rundunar sojin Rasha, cewar TheCable.
Rahotanni suka ce lauyoyinsa sun sanar da hukumomin Najeriya halin da yake ciki inda suka ce ya samu bizar yawon buɗe ido daga ofishin jakadancin Rasha da ke Abuja a ranar 16 ga Oktoban 2025.
A cewarsu, an yi masa alkawarin aikin tsaro ne kafin tafiyarsa wanda daga ya juya zuwa wani abu daban
Sai dai da isarsa Moscow, an kwace masa takardun tafiya tare da tilasta masa sanya hannu kan takardun shiga soja da aka rubuta gaba ɗaya da harshen Rashanci ba tare da mai fassara ba.
Daga baya ne ya gano cewa an riga an saka sunansa cikin rundunar sojin Rasha wanda lamarin ya daga masa hankali, cewar wani rahoton TVC News da aka wallafa a Instagram.

Source: Getty Images
A ina Adamu ya makale a Rasha?
Lauyoyinsa sun ce yanzu haka yana makale a wani sansanin soja bayan ya ƙi a tura shi fagen daga a yankunan yaƙi na Ukraine.
A ranar Alhamis, hukumar leƙen asirin tsaro ta Ukraine ta sanar da gano gawarwakin ’yan Najeriya biyu a yankin Luhansk.
An ce mutanen, Hamzat Kazeem Kolawole mai shekara 42 da Mbah Stephen Udoka mai shekara 38, sun mutu ne a ƙarshen Nuwamban 2025 bayan shiga rundunar sojin Rasha.
Binciken tashar talabijin ta CNN ya bayyana yadda ake zargin wasu ’yan Afirka daga Ghana, Najeriya, Kenya da Uganda ana yaudararsu da tayin ayyukan farar hula kafin daga bisani a tilasta musu shiga soja.
Sai dai, Rasha ta yi watsi da rahotannin, yana mai nesanta gwamnatin Kremlin da zargin shirye-shiryen ɗaukar ma’aikata ta hanyar yaudara.
Rasha ta magantu kan daukar 'yan Najeriya soja
Mun ba ku labarin cewa Gwamnatin Rasha ta fito ta yi magana kan rade-radin da ake yi cewa tana daukar 'yan Najeriya su je taya ta yaki a matsayin sojoji.
Jakadan kasar Rasha a Najeriya, Andrey Podyolyshev ne ya bayyana haka bayan an yada wasu rahotanni a baya kan lamarin.
Batun ya kara daukar hankali ne bayan bullar wani labari da ke nuna wani matashi daga Kano ya rasu yana taya Rasha yaki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

