Matashi Ya Bar Aikin Dan Sanda bayan Shekaru 12, Ya Koma Mai Renon Tsofaffi
- Wani matashi ɗan Ghana ya bar aikin ɗan sanda bayan shekaru 12, ya koma Birtaniya inda yake aiki a matsayin mai renon tsofaffi
- Ya ce rayuwa a Birtaniya ba sauƙi ba ce kamar yadda mutane ke zato, yana fuskantar tsadar haya da haraji, har ya ɗauki aiki na biyu
- Matashin ya shawarci matasa su yi tunani sosai kafin hijira, yana cewa kuɗin shiga yana raguwa sakamakon yawan biyan kuɗaɗe
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Accra, Ghana - Wani matashi ɗan Ghana mai suna Edward, ya jawo maganganu a kafofin sadarwa bayan ya watsar da aikin dan sanda da ya shafe shekaru 12.
Matashin wanda ya koma ƙasar Birtaniya ya ja hankalin mutane da dama bayan ya bayyana abubuwan da ya fuskanta tun bayan hijirarsa.

Source: UGC
Hakan na cikin wani bidiyo da aka yi hira da shi a kafar SVTV Africa da aka wallafa a YouTube wanda ya samu martanin mutane da dama.
Dalilin matashi na barin aikin dan sanda
Edward ya bayyana cewa ya yi aikin ɗan sanda a kasar Ghana tsawon shekaru 12, kafin ya yi murabus daga mukaminsa domin yin hijira zuwa Birtaniya don neman rayuwa mafi alheri.
Da isarsa Birtaniya, ya ce wata goggonsa ce ta taimaka masa, inda ta tallafa masa ya samu horo da takardun da suka ba shi damar fara aiki a matsayin mai renon tsofaffi.
Edward ya ce sabanin abin da mutane da dama ke zato, ba gaskiya ba ne cewa ana samun kuɗi cikin sauƙi a Birtaniya.
Ya bayyana cewa a wasu lokuta har nadama yake yi kan shawarar hijirarsa, musamman idan ya tuna irin matsayin rayuwar da yake da shi a Ghana.
Ya koka kan tsadar haya, inda ya ce bayan cire haraji, albashinsa ya kai fam 1,800, amma yana biyan fam 800 haya.

Source: Getty Images
Matashi ya fadi wahalar da yake sha a Birtaniya
Saboda haka, ya ce dole ya ɗauki wani aiki na biyu domin iya jure wa kuɗaɗen da yake kashewa a rayuwar can.
Edward ya ce:
“Mutane da yawa suna tunanin ana samun kuɗi cikin sauƙi a nan, amma kuɗin biyan bukatu na cin babban kaso na albashi.”
Ya kuma bayyana cewa kafin hijirarsa, yana gina gida a Ghana, kuma yana tunanin zai iya gina bene cikin ɗan lokaci bayan zuwa Birtaniya, amma ya ce hakan bai yiwu ba, don haka ya dakatar da aikin ginin.
Da aka tambaye shi dalilin da ya sa har yanzu yake Birtaniya duk da ƙalubalen, Edward ya ce yana da niyyar komawa Ghana, amma yana son ya fara tara kuɗi kafin dawowa.
Bayan wallafa rahoton, wasu sun ba shi shawara kan aure da tsara rayuwa, yayin da wasu ke cewa rayuwar ƙasashen waje na koya wa mutum darasi mai tsauri game da hakikanin rayuwa.
Yar Najeriya na samun makudan kudi a Birtaniya
Mun ba ku labarin cewa wata hazikar yar Najeriya da ke zama a Birtaniya ta bayyana yawan kudin da take samu daga aikin kula da mutane.
A cewar matashiyar, ana biyanta fam 100 a kullun kan aikin kula da mutum da take yi a Turai wanda ya jawo maganganu daga mutane.
A wani bidiyo da ta saki, ta yi jawabinta ne ga masu cin zarafi da ke mata ba'a kan aikin da take yi a kasar Birtaniya.
Asali: Legit.ng


