Sanata Ezea, da Wasu 'Yan Majalisar Tarayya 4 da Suka Mutu a cikin Watanni 18
- Okechukwu 'Okey' Ezea, dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Enugu ta Arewa a majalisar dattawa ya riga mu gidan gaskiya
- Marigayi Ezea ya lashe zabensa ne a karkashin LP, kuma shi ne kadai dan jam'iyyar da ya yi sauya a majalisar daga Enugu
- Baya ga Sanata Ezea, Legit Hausa ta tattaro jerin 'yan majalisar tarayya da suka rasu a watanni 18 (Mayun 2024 zuwa Nuwamba, 2025)
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - An sake shiga cikin jimami a siyasar Najeriya yayin da wani dan majalisar dattawa, Okey Ezea ya rigamu gidan gaskiya.
A safiyar Laraba, 19 ga Nuwamba 2025, iyalan Sanata Okey Ezea suka tabbatar da cewa sanatan Enugu ta Arewa North ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya.

Source: Twitter
Sanata Okey Ezea ya rasu a majalisa
A cikin wata sanarwa da ɗansa, Jideofor Ezea, ya fitar, an ji cewa sanatan ya rasu ne da misalin ƙarfe 11:07 na daren Talata, 18 ga Nuwamba 2025, a wani asibitin kudi a Legas, in ji rahoton Premium Times
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sanarwar, Jideofor Ezea ya bayyana cewa:
“Cikin bakin ciki da jimami muke sanar da rasuwar Sanata Okey Ezea, mai wakiltar Enugu ta Arewa a Majalisar Dattawa ta 10.
“Okey Ezea ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya, kuma har zuwa rasuwarsa ya kasance jigo a zauren majalisa.”
Masu sharhi na siyasa sun bayyana Ezea a matsayin ɗan majalisa mai tsayin daka wajen kare yankinsa, musamman kan batutuwan tsaro, tattalin arziki, da matsalolin habaka yankin Kudu maso Gabas.
2024-2025: 'Yan majalisar tarayya da suka rasu
Mutuwar Ezea ta ƙara yawan 'yan majalisar tarayya (majalisar wakilai da ta dattawa) da suka riga mu gidan gaskiya cikin shekaru biyu da suka gabata.
Ga jerin 'yan majalisar a kasa:
1. Isa Dogonyaro – Mayu 2024
Isa Dogonyaro, ɗan majalisar wakilai daga Babura/Garki (Jigawa), ya rasu yana da shekara 46, kamar yadda muka ruwaito.
Dan majalisar ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya a Abuja, kuma ya kasance fitaccen mai magana kan harkokin noma da cigaban kananan hukumomi.
2. Olaide Akinremi – Yuli, 2024
Olaide Akinremi na APC, mai wakiltar Ibadan ta Arewa, ya rasu yana da shekara 51, kamar yadda rahoton The Cable ya nuna.
Hon. Akinremi Jagaban ya kasance babban mai tallafa wa matasa da bunkasa kasuwanci a Oyo, kuma an yi rashin sa sosai a yankinsa.
3. Ekene Abubakar Adams – Yuli, 2024
Hon. Ekene Adams na jam’iyyar LP ya rasu yana da shekara 39, makonni kafin ya fara wani muhimmin kudiri kan tsaro a Kaduna.
Legit Hausa ta rahoto cewa, mutuwar Ekene Abubakar Adams ta girgiza jam’iyyar LP da mazabar da yake wakilta.
4. Ifeanyi Ubah – Yuli, 2024

Source: Twitter
A cikin watan Yulin 2024 majalisar dattawa ta rahoto cewa Sanata Ubah ya rasu a Landan bayan rashin lafiya yana da shekara 52.
Mun ruwaito cewa, Sanata Ifeanyi Ubah ya kasance ɗaya daga cikin fitattun ’yan siyasar Anambra masu ƙarfi a masana’antar mai.
5. Adewunmi Onanuga – Janairu, 2025
Mataimakiyar shugaban masu rinjaye ta majalisar wakilai, Adewunmi Onanuga, ta rasu bayan gajeriyar rashin lafiya.
Adewunmi Onanuga ta yi suna wajen kare haƙƙin mata, yara, da marasa galihu a lokacin da take wakilci, kamar yadda muka rahoto.
2025: Clark da 'yan siyasa 5 da suka mutu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, a tsakanin Janairu zuwa Maris din 2025, fitattun 'yan siyasar Najeriya biyar sun bakunci lahira, ciki har da Chief Edwin Clark.
Waɗannan fitattun mutane sun shafe shekaru da dama a harkokin siyasa, inda suka taka rawa wajen inganta tattalin arziki, zamantakewa da shugabanci a ƙasar nan.
Rasuwar 'yan siyasar, da suka hada da da Clark, Pa Ayo Adebanjo, Adewunmi Onanuga, Justice Azuka, Dr. Doyin Okupe ta bar babban gibi a siyasar Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


