'Yan Ta'adda na Yi wa Kiristocin Najeriya Kisan Kiyashi? Minista Ya Tsage Gaskiya

'Yan Ta'adda na Yi wa Kiristocin Najeriya Kisan Kiyashi? Minista Ya Tsage Gaskiya

  • Gwamnatin tarayya ta ce ba gaskiya ba ne cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi Najeriya, tana mai cewa an yi ikirarin don yaudara
  • Ministan yada labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa ’yan ta’adda suna kai hari ga kowa ba tare da la’akari da addini ko kabila ba
  • Fiye da ’yan ta’adda 13,500 aka kashe, kusan mutane 10,000 aka ceto daga 2023 zuwa 2025 a fadin kasar kamar yadda rahoto ya nuna

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Gwamnatin tarayya ta yi watsi da rahotanni daga wasu kafafen waje da masu yada labarai a intanet da ke ikirarin cewa ana kisan kiyashi ga Kiristoci a Najeriya.

A wata sanarwa da ministan bayanai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya fitar ranar Lahadi, 28 ga Satumba, 2025, gwamnatin ta ce wannan batu “karya ne, mara tushe kuma mai tada fitina.”

Kara karanta wannan

Magoya bayan Peter Obi sun tanka bayan ADC ta ba'yan hadaka umarni

Gwamnatin tarayya ta ce ba gaskiya ba ne cewa ana yiwa Kiristoci kisan kare dangi
Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris. Hoto: @HMMohammedIdris
Source: Twitter

'Ba a yi wa Kiristoci kisan kiyashi' - Idris

Sanarwar da Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X ta rahoto Mohammed Idris ya ce bayyana matsalar tsaro a matsayin hari na musamman kan Kiristoci yaudara ce da kuma taka rawa wajen ciyar da burin ’yan ta’adda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa hare-haren ’yan ta’adda suna shafar Musulmai, Kiristoci da ma wadanda ba su da addini, ba tare da nuna wani bambanci ba.

"Yayin da Najeriya, kamar sauran wasu kasashe, ke fama da matsalar tsaro, cewa ana kai hare-haren ne kacokan kan Kiristoci karya ce zagoronta, kuma zai haddasa matsala.
"Ta'addancin 'yan ta'adda bai kyale wani addini ko yare ba. Wadannan 'yan ta'addan suna farmakar mutane ne ba tare da la'akari da wane Musulmi ne ko Kirista ba, su ba ruwansu da addinin mutane."

- Mohammed Idris.

Yaki da ta'addanci da hadin kan addini

Gwamnatin ta ce tsakanin Mayun 2023 zuwa Fabrairun 2025, fiye da ’yan ta’adda da masu laifi 13,543 aka kashe, kusan mutane 10,000 kuma aka ceto daga hannunsu.

Kara karanta wannan

Bulama Bukarti ya hango matsaloli a sulhu da ƴan ta'adda, ya ba gwamnati shawara

A watan da ya gabata, manyan shugabannin kungiyar ANSARU — reshen Al-Qaeda a Najeriya — sun shiga hannu a wani samame na sojoji, ciki har da shugaban kungiyar Mahmud Muhammad Usman da mataimakinsa Mahmud al-Nigeri.

Ya ce an gurfanar da akalla rukunai bakwai na wadanda ake zargi da Boko Haram, inda sama da mutane 700 aka samu da laifi, ana kuma ci gaba da shari’o’i a yanzu.

Mohammed Idris ya ce Najeriya na alfahari da kasancewa kasa mai dauke da Musulmai da Kiristoci da yawa, inda kuma shugabannin rundunar soji da na ’yan sanda duka Kiristoci ne a yanzu.

Ministan yada labarai ya ce 'yan ta'adda ba sa la'akari da addini ko kabilanci wajen kai hari.
Hoton ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris. Hoto: @HMMohammedIdris.
Source: UGC

Kira ga kafafen yada labarai

Ya ambaci karramawar da aka yi wa malamai biyu na Najeriya, Fasto James Wuye da Imam Muhammad Ashafa, wadanda suka lashe lambar yabo ta Commonwealth Peace Prize a 2025 saboda kokarinsu na kawo sulhu tsakanin Musulmai da Kiristoci.

Ministan ya ce labarin Najeriya ba na kisan kiyashi ba ne, illa labari ne na juriya, hadin kai da zaman lafiya.

Ya bukaci kafafen yada labarai na waje da sauran masu magana su guji yada kalaman rarrabuwar kawuna, su kuma tallafa wa kokarin Najeriya wajen yaki da ta’addanci.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An yi kutse a shafin gwamnatin Najeriya, an wallafa wata takarda

'Kisan kiyashi': Atiku ya yi magana

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya yi Allah wadai da sabon harin da mayakan Boko Haram su ka kai Borno.

Atiku Abubakar ya ce lokaci ya yi da ƴan Najeriya za su tashi tsaye wajen yaƙi da ta’addanci domin a kawo karshen kisan gillar 'yan ta'adda.

Babban jagoran 'yan adawar ya yi ta’aziyya ga gwamnan Borno, Babagana Zzulum da iyalan mutanen da Boko Haram ta kashe a karshen makon jiya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com