An Ji Kunya: Magidanci Ya Kai Karar Saurayin Diyarsa Kotu kan 'Abin Duniya' a Kaduna
- Wani magidanci ya kai karar saurayin diyarsa gaban kotu a jihar Kaduna saboda zargin satar kudin gadon matarsa
- A zaman shari'ar da aka yi, mai gabatar da kara ya ce saurayin ya yaudari yarsa, ya cire makudan kudi na gadon matarsa daga asusunta
- Wanda ake tuhuma, Yunana Zock ya ce dama ya na ajiye kudi a asusun budurwarsa kasancewar suna zaune a wuri da a Abuja
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kaduna - Rigima ta barke tsakanin wani magidanci da saurayin diyarsa kan kudin gadon matarsa wacce ta mutu a jihar Kaduna.
Magidancin mai suna, Ishaku Joseph ya kai karar saurayin ‘yarsa, Yunana Zock, gaban kotu a jihar Kaduna bisa zargin sace kudin fanshon matarsa da ta rasu.

Source: Getty Images
Magidanci ya kai karar saurayin diyarsa
Mai gabatar da ƙara, ASP Jeremiah Amfani, ya shaida wa kotu cewa wanda ake tuhuma ya yaudari ‘yar Joseph mai suna Emmanuella, in ji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya shaidawa alkali cewa saurayin ya kwashe kudaden da suka kai Naira miliyan 13 da aka biya a matsayin fanshon mamaciyar watau matar Joseph.
Dan sandan ya bayyana cewa kudin an tura su cikin asusun Emmanuella a shekarar 2023, kasancewar ita ce aka ayyana a matsayin mai gadon mahaifiyarta.
Joseph ya kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda, inda aka gudanar da bincike kafin gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban kuliya.
Yadda saurayin ya yaudari Emmanuella
A lokacin da take bada shaida a gaban kotu, Emmanuella ta ce saurayinta ya dauki katin ATM ɗinta ba tare da ta sani ba, sannan ya cire kudin daga asusun bankinta.
Amma a nasa bangaren, Yunana Zock ya ce tun farko ya yi ajiyar kusan Naira miliyan 11.9 a asusun budurwarsa.
Sannan ya kara da cewa budurwar tasa ta masa alkawarin cewa za ta ba shi Naira miliyan 2 domin ya fara sana’a.
Yunana Zock ya shaida wa alkalin cewa sun zauna wuri daya da budurwarsa a birnin Abuja, wanda hakan ya sa kowa ya san lambobin sirri na ATM din kowa.

Source: Facebook
Saurayi ya fara gabatar da shaida a kotu
Zock ya gabatar da wata takarda da ke nuna bayanin asusun bankinsa na Opay, wanda kotu ta karɓa a matsayin shaida.
Ya kuma sanar da kotu cewa zai gabatar da shaidar mutum guda a zaman shari’ar gaba, kamar yadda Daily Post ta kawo.
Alƙalin kotun, Mai shari'a Patience Musa, ta dage zaman sauraron shari’ar zuwa ranar 30 ga watan Satumba, 2025 domin bai wa wanda ake tuhuma damar ci gaba da kare kansa.
Budurwa ta mutu a dakin wanda za ta aura
A wani labarin, kun ji cewa wata budurwa mai shekara 24 da haihuwa, Kelechi Ebubechukwu, ta mutu a dakin saurayin da za ta aura.
An tsinci gawar Kelechi Ebubechukwu a dakin saurayin nata ne da ke Gwagwalada, kuma ana kyautata zaton ta mutu ne a ranar Talata.
Rahotannin farko na binciken da yan sanda auka gudanar, sun nuna cewa an gano wasu magunguna a dakin da ta mutu, amma babu alamar rauni jikin marigayiyar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

