Jarumin Fim, Don Richard Ya Talauce, Yana Neman Taimakon N30m daga 'Yan Najeriya

Jarumin Fim, Don Richard Ya Talauce, Yana Neman Taimakon N30m daga 'Yan Najeriya

  • Jarumin Nollywood, Don Richard ya ce matarsa ta gudu ta bar shi saboda tsananin talauci, wanda ta kai ya sayar da motarsa
  • Yayin da ya nemi taimako daga 'yan Najeriya, jarumin ya ce yana bukatar Naira miliyan 30 don jinyar rashin lafiyar da ke damunsa
  • Don Richard ya ce ya kamu da ciwon koda ne shekaru biyu bayan da ya daina shan sigari da giya, abin da ya jefa shi a damuwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Fitaccen ɗan fim ɗin Nollywood, Don Richard, ya roƙi ‘yan Najeriya da su taimaka masa da kuɗi yayin da yake fama da matsanancin rashin lafiyar koda da kuma talauci.

A wata hira mai cike da tausayi da yayi da jaruma Biola Bayo, Don Richard ya bayyana cewa sai da ya sayar da motarsa kan N1.5m saboda tsananin wahalar rayuwa.

Kara karanta wannan

'Ban da Peter Obi': An yi wa Malami wahayi game da mutum 3 da za su fatata a 2027

Jarumin Nollywood, Don Richard ya talauce, yana neman kudi don jinyar kansa
Jarumin Nollywood, Don Richard na neman taimakon N30m daga 'yan Najeriya. Hoto: @donrichard
Source: Instagram

Matar jarumin fim ta gudu saboda talauci

Ya kuma tuna lokacin da ya fara aikin fim da yadda ya rika karade Legas a kafa, daga Bariga zuwa Chemist, Unilag, Iwaya, Sabo, Yaba da Ojuelegba, inji rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa matar da ya aura ta gudu ta bar shi saboda talaucinsa, yana mai cewa:

"Na fito waje wata rana sai na ga matata, na fashe da kuka. Na ce da ita, 'Maman 'yan biyu, wani namijin ne kuma ya yi sa'ar samunki yanzu?' Ta guje ni ne saboda na talauci."

'Dan wasan fim yana neman taimako

Don Richard ya ce yana bukatar Naira miliyan 30 don jinya, adadin da ya ce ya fi ƙarfin aljihunsa, yana mai cewa:

“Likita ya gaya mani gaskiya game da rashin lafiya ta, na ji tsoro matuka. Na ce, ‘Ya Ubangiji, ni ban da kuɗi, kai ne sirrina. Idan ka juya mani baya, to za su ganni a rana."

Kara karanta wannan

'Yadda matata ta hana ni sukar Buhari bayan ya mutu': Tsohon gwamna ya magantu

Biola Bayo ta ɗauki nauyin taimaka masa ta hanyar wallafa bayanansa a Instagram, inda take roƙon masu hannu da shuni da su ba da gudunmawarsu domin ceto rayuwarsa.

Don Richard ya ce ya fara ciwon ne shekaru biyu bayan da ya daina shan sigari da giya, yana mai mamakin yadda rashin lafiyar ta same shi duk da canjin salon rayuwarsa.

Ya shawarci mutane da kada su yi tunanin cewa lafiyarsu kalau take saboda kawai suna jin daɗin jiki, yana mai jaddada muhimmancin duba lafiya lokaci zuwa lokaci.

Don Rechard ya ce ya daina shan sigari da giya amma ya kamu da cutar koda
Jarumin Nollywood Don Richard ya kamu da rashiya lafiya, kuma yana fama da talauci. Hoto: @donrichard
Source: Instagram

Tarihin rayuwar Don Richard a takaice

Jaridar Tribune ta rahoto cewa an haifi jarumin na fim Don Richard a jihar Ondo, ya kuma girma a yankin Bariga da ke Legas.

Ya fara aikin fim tun 1989 a matsayin mai taimakawa wajen shirya shirye-shiryen NTA Channel 10 kafin ya koma harkar fim da koyarwa.

Yana da digiri na biyu daga Jami’ar Legas kuma ya fito a fina-finai kamar The Darkness, Man in the Jungle, da fina-finan Yarbanci kamar Elede da Inujin.

Don Richard ya shahara da fina-finansa a Nollywood kuma ya yi suna a matsayin mai shirya fim da kuma mai horar da matasa kan harkokin nishadi..

Kara karanta wannan

An yi rashi: Fitaccen ɗan wasan kokowa na duniya, Hogan ya mutu yana da shekaru 71

Tsohuwar jaruma, Mansura ta talauce

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan damfara sun kwashe gaba daya kudin da ke a cikin asusun bankunan tsohuwar jarumar Kannywood, Mansura Isah.

Tsohuwar matar Sani Danja, ta sanarwa duniya halin da take ciki bayan 'yan damfara sun sace duk wani kudi da ta mallaka a banki baki daya.

Yayin da ta ce ta talauce yanzu, Mansura Isah ta aika sako ga wadanda ta yi alkawarin za ta ba su tallafi tana mai nuna damuwa kan rashin samun wanda zai taimaka mata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com