'Yan Najeriya 6 Sun Shiga Jerin Bakaken Fata Mafi Kudi a Duniya, Dangote ne a gaba
Aliko Dangote, attari mafi arziki a Afrika, Femi Otedola, shugaban kamfanin First HoldCo, da wasu 'yan Najeriya hudu, sun shiga jerin bakaken fata mafi kudi a duniya a 2025.
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
A jadawalin mutane mafi kudi a duniya na 2025 da mujallar Forbes ta fitar, an ce bakaken fata 23 ne kacal a cikin attajirai 3,028 da suka tara biliyoyin daloli a duniya.

Asali: UGC
An fitar da jerin attajirai mafi kudi a duniya
A rahoton da mujallar Forbes ta fitar a shafinta na intanet, ta bayyana cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Bakaken fata 23 ne kawai suka samu shiga cikin jerin attajiran duniya a bana, kimamin kashi 0.8% kacal, kuma suna da tarin dukiya da tasiri a duniya.
"Gaba daya, wadanda bakaken fata 23 sun tara dukiyar da ta kai darajar dala biliyan 96.2, kuma sun fito daga fannin hada-hadar kudi, makamashi da fasaha."
Mujallar ta ce daga cikin wadannan bakaken fata 23 da suka tara biliyoyin daloli, shida daga cikinsu 'yan Najeriya ne.
'Yan Najeriya 6 mafi kudi a bakaken fata
Ga jerin attajiran Najeriya shida da suka shiga jadawalin Forbes na masu kudin duniya a 2025:
1. Aliko Dangote
Bisa ga rahoton mujallar, Dangote, wanda shi ne shugaban rukunonin kamfanin Dangote, shi ne kan gaba a wannan jeri, inda ya mallaki dala biliyan 23.9.
Mujallar ta ce arzikin Dangote ya yi tashin gwauron zabi ne yayin da matatar Dangote ta fara aiki a farkon shekarar 2024.
Daga farkon 2024 zuwa Maris a 2025, mujallar ta ce darajar dukiyar Dangote ta karu da dala biliyan 10.5 sakamakon fara aikin matatar man sa.
2. Mike Adenuga
Mike Adenuga ba boyayye ba ne a Najeriya da Afrika baki daya, shi ne mamallakin Globacom, wani kamfanin sadarwa a Najeriya.
A jerin bakaken fata mafi kudin a duniya na 2025 da suka fito daga Najeriya, Adenuga ne na biyar da dukiyar da ta kai darajar dala biliyan 6.8.
3. Abdulsamad Rabiu
Mai bin bayan Mike Adenuga a jerin bakaken fata mafi kudi a duniya daga Najeriya shi ne Abdulsamad Rabiu, wanda ya kafa rukunonin kamfanin BUA.
Abdulsamad BUA shi ne na shida, bayan ya mallaki dukiyar da darajarta ta kai dala biliyan 5.1, kuma shi ne na 3 a mafi kudi a Najeriya.
4. Adebayo Ogunlesi
Wani ɗan Najeriya da ke cikin jerin shi ne Adebayo Ogunlesi, shugaban kamfanin Global Infrastructure Partners (GIP), wanda ya mallaki dukiyar da ta kai darajar dala biliyan 2.2.
Forbes ta bayyana cewa Ogunlesi shi ne bakar fata na 11 a mafi kudi a duniya.
A watan Oktobar shekarar 2024, Ogunlesi ya sayar da GIP ga kamfanin BlackRock kan dala biliyan 12.5, aka biya shi da tsabar kudi da kuma hannun jari.
5. Femi Otedola
Wanda ya zo a matsayin na 12 a wannan jeri shi ne Femi Otedola, shugaban kamfanin Geregu, inda ya mallaki dukiyar da darajarta ta kai dala biliyan 1.5.

Kara karanta wannan
Najeriya ta yi rashi: Yadda Edwin Clark da fitattun ƴan siyasa 4 suka mutu a 2025
Mujallar Forbes ta ce Otedola ya mallaki dukiyarsa ne daga saye da sayar da kayayyaki kafin daga bisani ya sayar da hannun jarinsa na kamfanin Forte Oil ya shiga harkar makamashi.
"A yau, shi ne shugaba kuma wanda ke da karfin iko a Geregu Power, wani kamfani da ke samar da makamashi, da masu hannun jari a cikinsa suka hada da gwamnatin Najeriya da hukumar makamashi ta China."
- A cewar rahoton mujallar.
6. Tope Awotona

Asali: UGC
Tope Awotona ne dan Najeriya na karshe a jerin bakaken fata da suka fi kowa kudi a duniya a 2025.
Rahoton mujallar ya nuna cewa, a 2013, Awotona ya samar da Calendly, wani kamfanin fasahar na'ura mai kwakwalwa, wanda masu zuba jari suka kiyasta darajarsa zuwa dala biliyan 3 a 2021.
Tope Awotona shi ne ya zo na 14 a cikin bakaken fata 23 da suka shiga jerin masu kudin duniya, bayan ya tara dukiyar da ta kai dala biliyan 1.4.
Adenuga ya shiga gaban BUA a tarin dukiya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Mike Adenuga, mamallakin kamfanin Globacom, ya shiga gaban Abdulsamad Rabiu BUA, a jerin masu kudin Najeriya.
Mista Mike Adenuga ya shiga gaban shugaban rukunonin kamfanin BUA ne a 2024 bayan da arzikinsa ya karu zuwa dala biliyan 7.4, sakamakon ribar Globacom.
Asali: Legit.ng