Sanata Natasha Ta Zargi Akpabio da Taba Mata Jiki, da Yi Mata Kalaman Batsa

Sanata Natasha Ta Zargi Akpabio da Taba Mata Jiki, da Yi Mata Kalaman Batsa

  • Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta zargi shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da yi mata maganganu masu muni
  • Akpoti ta yi zargin cewa an dakatar da ita daga majalisa ne domin a hana ta fadin gaskiya game da cin zarafin da ake yi mata
  • Sai dai Majalisar dattawan Najeriya ta musanta zargin da Sanata Akpoti-Uduaghan ke yi wa Akpabio da dalilin dakatar da ita

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kogi - Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta zargi shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da yin maganganun cin zarafin mata a kanta.

Sanatar ta yi magana ne yayin da ake cigaba da takaddama kan dakatar da ita da aka yi da shari'a da suke bugawa a kotu.

Kara karanta wannan

Zargin lalata: Sanata Natasha ta tafi Birtaniya, ta sake tono wani 'sirrin' Akpabio

Natasha
Natashi ta zargi Akpabio da mata kalaman cin zarafi. Hoto: Nigerian Senate
Asali: Twitter

A wata hira da ta yi da BBC, Akpoti-Uduaghan ta bayyana cewa Akpabio na yawan yi mata kalamai masu alamar cin mutunci a lokuta daban-daban, har ma a gaban wasu sanatoci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Natasha ta yi zargin cewa a wani lokaci har matsa mata hannu da nufin nuna mata soyayya Akpabio ya yi.

Kalaman da Natasha ta ce Akpabio ya fada

Jaridar the Cable ta wallafa cewa Sanatar ta bayyana wasu daga cikin maganganun da ta ce Akpabio ya yi mata.

“Wata rana na manta ban sanya zoben aure na ba, saboda na yi gaggawar zuwa aiki. Sai Akpabio ya ce: ‘Oh Natasha, ba ki sanye da zobenki…
"Wannan alama ce ta neman kulawa ta musamman?’”

Haka zalika, ta ce wani lokaci Akpabio ya yi wata magana a gabanta da wasu Sanatoci, yana cewa:

“Natasha, daga ganin kunkuminki, mijinki yana jin dadinki”

Kara karanta wannan

Zargin lalata: Sanata Natasha ta kasa hakura, ta sake sabuwar fallasa kan Akpabio

Ta ce bayan irin wadannan maganganu game da kugunta, sanatocin da ke wurin kan yi dariya, su wuce kamar ba a ce komai ba.

Sanata Natasha ta fashe da kuka yayin bayani

A cikin hirar, Natasha Akpoti-Uduaghan ta fashe da kuka lokacin da aka tambaye ta yadda kalaman da ake mata ke shafar ta.

“Mutane ba su fahimta ba. Wata kila ba mu fiye tattauna irin wannan matsalar a Najeriya ko Afrika ba,”

- Sanata Natasha Akpoti

Ta ce abin takaici ne yadda ake cin zarafin mata a siyasa, musamman a wuraren da maza suka mamaye, amma sai a wulakanta mace idan ta fadi ra’ayinta.

Sai dai, ta ce ta samu karfafa gwiwa daga wasu mata ‘yan majalisa daga kasashen Afrika da suka kirata domin nuna mata goyon baya.

Shugaban majalisa
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio. Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Majalisar dattawa ta musanta zargin Natasha

Mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Onyekachi Nwaebonyi, ya mayar da martani yana cewa babu wata shaida da ke nuna cewa Akpabio ya taba yin haka.

Kara karanta wannan

"Majalisa ta koma kamar kungiyar asiri," Natasha ta fadi abin da Sanatoci ke tsoro

Ya bayyana cewa shugaban majalisar dattawa bai taba yi wa Natasha Akpoti wani furuci maras kyau ba, ko a cikin majalisa ko a wani wuri na daban.

Kotu ta ba majalisa damar dakatar da Natasha

A wani rahoton, kun ji cewa Kotun tarayya da ke Abuja ta ja da baya kan hukuncin hana majalisa dakatar da Sanata Natasha Akpoti.

Bayan yanke hukuncin, kotun ta bayyana cewa hakan ba zai shafi karar da Natasha Akpoti ta shigar da wasu 'yan majalisar ba kan zargin neman lalata da ita.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng