Ridda: Adam A Zango Ya Nuna Yatsa ga Babban Malamin Izala, Sheikh Burhan
- Malamin Musulunci a kungiyar Izala mai hedikwata a Jos, Sheikh Al-Burhan ya ce rawa da alkyabba na iya fitar da mutum daga Musulunci
- Dan wasan kwaikwayo, Adam A. Zango ya mayar da martani ta hanyar wallafa bidiyon Larabawa da shi kansa yana rawa da alkyabba
- Martanin Adam Zango ya haddasa ce-ce-ku-ce tsakanin mutane da dama a kafafen sada zumunta inda aka bayyana ra'ayoyi daban daban
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Sabon ce-ce-ku-ce ya barke bayan da fitaccen malamin Izala, Sheikh Salihu Alburhan, ya yi bayani kan abin da ke iya fitar da mutum daga Musulunci.
A cikin wa'azinsa, Sheikh Burhan ya ce sanya alkyabba sannan a yi rawa yana daga cikin abubuwan da ke fitar da mutum daga addini, domin a cewarsa, alkyabba sifa ce ta annabawa.

Asali: Facebook
Fitaccen dan fim a Najeriya, Adam A. Zango ya yi martani ga malamin a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Martanin Adam A. Zango ya sanya dubban mutane tofa albarkacin bakinsu a kafafen sada zumunta.
Martanin Adam Zango ga Sheikh Burhan
Bayan kalaman Sheikh Burhan, Adam A. Zango ya wallafa bidiyo a shafinsa na sada zumunta, yana nuna wasu Larabawa sanye da alkyabba suna rawa.
Baya ga hakan, jarumin ya kuma wallafa bidiyon kansa yana rawa da alkyabba, wanda hakan ke nuni da cewa bai yarda da fatawar malamin ba.
Bugu da ƙari, Adam Zango ya rubuta cewa:
"Allah da zuciya yake aiki Malam, ba da sutura ba."
Ce-ce-ku-ce bayan martanin Adam Zango
Bayan martanin, mutane da dama sun bayyana ra’ayoyinsu kan batun, wasu na goyon bayan Sheikh Burhan, wasu kuma na ganin ya yi tsauri.

Kara karanta wannan
Tinubu ya gana da Aminu Ado Bayero, ya ba shi tabbacin kawo karshen matsaloli a Kano
Zainab Sulaiman Romo ta ce:
"Maganar ta yi tsauri da yawa, Malam. Ridda ba abu ne mai sauki ba. Idan ma akwai wannan magana, akwai buƙatar a duba ta sosai, domin ba da ijma'in malamai aka yanke hakan ba."
Kabiru Yahaya Abdullahi ya mayar da martani ga Adam Zango, yana cewa:
"Kai ne zaka fada masa Allah da zuciya yake aiki? Ko hadisi daya ba ka da shi a kanka amma har kana iya yin raddi ga malamin addini?"
Mukhtar Abubakar Mahmud ya ce:
"Kada ka zama mai jin jayayya da kowanne furuci. Sannan ka zama mai karbar gyara."
Lawal Salisu Lamido ya yi addu’a yana cewa:
"Allah ya shiryar da mu bisa sunnar AnnabinSa."
Ubayo Maigari Dukiya ya ce:
"Ni ma dai ban fahimci me Malamin nan yake nufi ba. Daga saka alkyabba in ka yi rawa ka kafirta? Me ya sa wasu malaman suke gaggawar kafirta mutane?"

Kara karanta wannan
Dambarwar Albany da abubuwa 4 da suka ta da kura a kafofin sadarwa a Arewacin Najeriya
Ashiru Aminu Mai Taru ya yi gargadi ga Adam Zango, yana cewa:
"Bai kamata kayi sharing bidiyo tare da malamin ba, koda kuwa kai yake nufi. Wannan ba daidai ba ne.
"Idan kaji kamar abin da yake fada ba daidai ba ne, ka nemi malaminka ka tambaya. Allah shi ne masani."
Nasarorin da aka samu a cibiyar Albani
A wani rahoton, kun ji cewa cibiyar da Albani Zariya ya asassa ta fitar da rahoto kan nasarorin da ta samu cikin shekaru 11.
Shugabannin Darul Hadthis Salafiyya da ke Zariya sun ce an samu nasarori da suka hada da fadada wurare da dama, fara gina asibitin Albani da sauransu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng