Abin da Khalifan Inyass Ya Fadawa Tinubu game da Samun Goyon Bayan 'Yan Tijjaniyya

Abin da Khalifan Inyass Ya Fadawa Tinubu game da Samun Goyon Bayan 'Yan Tijjaniyya

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi sallar Juma’a tare da shugabannin darikar Tijjaniyya a Masallacin fadar Aso Villa a Abuja
  • Khalifa Sheikh Muhammad Mahi Inyass ya yi wa Najeriya addu’o’in zaman lafiya da ci gaba yayin da ya jagoranci jama'a zuwa fadar
  • A daya bangaren, mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima, ya yi sallar Juma’a a masallacin kungiyar Izala a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi sallar Juma’a tare da shugabannin darikar Tijjaniyya a Masallacin Aso Villa da ke Abuja a ranar Juma’a.

Jagoran tawagar darikar Tijjaniyya, Khalifa Sheikh Muhammad Mahi Inyass, shi ne ya jagoranci tawagar, inda suka yi addu’o’in samun albarka, zaman lafiya, da ci gaban Najeriya.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya yi sallar Juma'a tare da manyan malaman Tijjaniyya, an ji abin da suka tattauna

Tijjaniyya
Tinubu ya gana da shugannin Darikar Tijjaniyya. Hoto: Federal Ministry of Information and National Orientation, Nigeria
Asali: Facebook

Ma'aikatar yada labarai da wayar da kan al'umma ce ta wallafa yadda sallar ta gudana a fadar shugaban kasa a shafinta na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron ya biyo bayan ziyarar da shugabannin Tijjaniyya suka kawo Najeriya domin bikin Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass wanda ya kasance cikin manyan jagororin Tijjaniyya.

Khalifan Inyass ya yi wa Najeriya addu’a

Khalifa Sheikh Muhammad Mahi Inyass ya bayyana jin dadinsa kan yadda Shugaba Tinubu ke tafiyar da mulki, yana mai addu’ar Allah ya kara masa hikima da nasara.

Khalifa Inyass, wanda shi ne ɗan fitaccen jagoran darikar Tijjaniyya ya bayyana cewa dalilin zuwansu Najeriya shi ne bikin Mauludin Inyass.

Premium Times ta rahoto cewa Khalifan ya ce taron ya kara karfafa hadin kai tsakanin mabiya darikar a Najeriya da ma duniya baki daya

Ya kuma tabbatar wa shugaba Tinubu da cikakken goyon bayan al’ummar Musulmi, musamman mabiya darikar Tijjaniyya miliyan 400 da ke Najeriya, Afirka ta Yamma da sauran sassan duniya.

Kara karanta wannan

APC ta yi kaca kaca da Atiku Abubakar, ta fadi wanda ke haddasa rikici a PDP

Tawagar Tijjaniyya ta yabawa Bola Tinubu

Shugabannin darikar Tijjaniyya da suka halarci taron sun yaba wa shugaba Tinubu kan yadda yake kokarin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban kasa.

Har ila yau, shugabannin sun bukaci al’ummar Najeriya da su ci gaba da yin addu’a domin fatan alheri ga kasa da shugabanninta.

Shettima ya yi sallah a masallacin Izala

A yayin da Shugaba Tinubu ke sallar Juma’a tare da shugabannin Tijjaniyya a Fadar Gwamnati, Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya halarci sallar Juma’a a Masallacin Izala.

Sanata Kashim Shettima ya wallafa a Facebook cewa ya halarci sallar Juma'a a masallacin Umar Bin Khattab da ke Utako, Abuja.

Bayan kammala sallar, Shettima ya halarci daurin auren wasu ma’aurata guda biyu – Shafi’u Ibrahim Sharif da Fatima Muh’d Kachalla, da kuma Yahaya Usman da Aisha Musa Mohammed.

NEF ta bukaci a saki Farfesa Yusuf

Kara karanta wannan

'Haba Malam': Hadimin Tinubu ya zargi El Rufa'i da neman rusa gwamnati kan sukar APC

A wan rahoton, kun ji cewa kungiyar dattawan Arewa (NEF) ta bukaci gwamnatin tarayya ta saki tsohon shugaban NHIS, Farfesa Usman Yusuf.

Legit ta ruwaito cewa hukumar EFCC ce ta kama Farfesa Usman Yusuf a gidansa da ke Abuja a ranar Labara kan wasu zarge zarge.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel