Mukaila Senwele: Fitaccen Mawakin Najeriya Daga Arewa Ya Rasu, An Yi Masa Sutura

Mukaila Senwele: Fitaccen Mawakin Najeriya Daga Arewa Ya Rasu, An Yi Masa Sutura

  • Allah ya yiwa fitaccen mawakin Yarbawa, Omotoso Mukaila Ayinla, wanda aka fi sani da Senwele a ranar Juma'a a jihar Legas
  • Mukaila Ayinla, ya kasance haifaffen dan jihar Kano wanda ya shahara a wakokinsa na zambo a salon wakar gargajiya ta Dadakuada
  • Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta yi bayanin yadda mawakin ya rasu bayan ya fito daga gidan shakatawa da 'yan uwansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kwara - Rahotanni sun bayyana cewa, Omotoso Mukaila Ayinla, fitaccen mawakin Yarbawa wanda ke rayuwarsa a jihar Legas ya rigamu gidan gaskiya.

An ce Omotoso Mukaila Ayinla, wanda aka fi sani da Senwele kuma dan asalin jihar Kwara ya rasu ne ranar Juma'a da daddare bayan gajeruwar jinya.

Fitaccen mawaki dan asalin jihar Kwara ya rigamu gidan gaskiya
An sanar da rasuwar fitaccen mawakin Yarbawa, Senwele a jihar Legas. Hoto: @Mukailasenwele5
Asali: Facebook

A cewar wata majiya da ta zanta da jaridar TheCable a ranar Asabar, mawakin barkwanci, Senwele ya fita da abokai da 'yan uwansa zuwa wajen shakatawa ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda fitaccen mawakin Najeriya ya rasu

Majiya ta ce bayan ya rabu da abokan tafiyarsa, sai ya fara korafin ba ya jin dadin jikinsa wanda ya a aka garzaya da shi asibiti, amma ya rasu a kan hanya.

Majiyar ta shaida cewa kafin rasuwar mawaki Senwele, ba shi da wata matsala ta rashin lafiya da za a ce ita ce silar rasuwarsa.

"Ya fita ne domin ya shakata tare da abokai da wasu 'yan uwansa. Sun bar wajen shakatawar tare inda ya nufi gidansa," a cewar majiyar.

Majiyar ta ci gaba da cewa:

"Sauran 'yan uwansa ba su isa gidajensu ba aka kira su aka sanar da su cewa Mukaila ya kamu da rashin lafiyar farat daya, inda suka garzaya suka dauke shi zuwa asibiti.
"Suna a kan hanyarsu ta zuwa asibitin ne mawakin ya ce 'ga garinku nan."

Senwele ya yi kaurin suna a wakokin Dadakuada

An rahoto cewa Senwele ya yi kaurin suna da wakokinsa na gargajiyar Dadakuada. An ce Dadakuada wani nau'in wakar Yarbawa ne.

Kara karanta wannan

2Baba: Fitaccen mawakin Najeriya ya saki matarsa, ya yi karin bayani a cikin bidiyo

An samo asalin wakar Dadakuada daga garin Ilorin na jihar Kwara kuma wani nau'in waka ne da ake amfani da shi wajen yin zambo cikin raha.

An ce mawakin ya yi amfani da wannan salon wakar wajen yiwa mutane zambo da gugar zana cikin raha yayin da ya ke magana kan batutuwa masu sarkakiya.

Mawakin ya wallafa bidiyo kafin rasuwarsa

Ko kafin rasuwarsa, an ce Senwele ya yi amfani da shafukansa na sada zumunta inda har ya yi rubutu a shafinsa na Instagram yana cewa "komai na tafiya dai-dai a wannan daren."

Ya kuma wallafa wani bidiyonsa da ya dauka a wajen wani wasa shekarar daya da ta gabata.

Kamar yadda ya wallafa wani bidiyon kwanaki uku da suka wuya inda aka ji yana korafi kan halin matsin da ake ciki a kasar nan.

Mawaki ya ba 'yan Najeriya shawara kafin rasuwarsa

Marigayin ya bukaci 'yan Najeriya da su yi duk mai yiwuwa don sanya farin ciki a rayuwarsu ko da kuwa suna fuskantar matsin tattalin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su

Haka kuma ya ba 'yan kasar shawarar kalubalantar shugabancin gwamnatin tarayya na gazawa wajen samar da sauki ga talaka.

An rahoto cewa an yi jana'iza tare da binne gawar Senwele a safiyar ranar Asabar kamar yadda addinin Musulunci ya tanar da gidansu da ke jihar Kwara.

Jarumar Nollywood ta kamu da cutar sepsis

A wani labarin, mun ruwaito cewa jaruma Omowunmi Dada ta kamu da cutar sepsis yayin daukar fim a Oyo, inda aka bar ta a otal ba tare da an kula da ita ba.

Jaruma Omowunmi Dada ta ce abin takaici ne yadda masu shirya fim din sun bukaci ta dawo musu da kudin aikin da ba ta karasa ba, duk da halin rashin lafiyarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.