Malamin Jami'a Ya Yi Zarra, Farfesa Ya Haddace Kur'ani Yana Shekaru 59
- Farfesa Tajudeen Yusuf na Jami’ar Legas da ya kware a fannin Inshora ya kammala haddace Alkur’ani mai girma duk da jadawalin aikinsa mai cike da dawainiya
- Wani limami kuma shugaban cibiyar Khalwatu Tanzeel, Dr AbdulHakeem AbdulLateef ya bayyana farin cikin da ya ji kan lamarin
- Farfesa Yusuf ya yi kira ga al'ummar Musulmi da su ba da muhimmanci ga hadda da fahimtar Alkur’ani ko da suna cikin dawaniyoyi daban daban
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Lagos - Farfesa Tajudeen Yusuf, kwararre a fannin Inshora a Jami’ar Legas, ya kafa sabon tarihi a rayuwarsa yayin da ya kammala haddace Alkur’ani mai girma a shekararsa ta 59.
An yabawa malamin jami'ar bisa kwarewa da jajircewa da ya nuna duk da dawainiyar da aikinsa ke tattare da shi.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su

Asali: Facebook
Limami kuma shugaban cibiyar Khalwatu Tanzeel, wacce ke koyar da harshen Larabci da Alkur’ani a Legas, Dr AbdulHakeem AbdulLateef ne ya wallafa labarin a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dr AbdulHakeem ya nuna farin cikinsa da godiya ga Allah bisa nasarar Farfesan, yana mai yaba masa bisa jajircewar da ya yi.
Malamin jami'a ya haddace Kur'ani
Dr AbdulHakeem AbdulLateef ya nemi a taya shi murna yayin sanar da haddar da Farfesa Tajudeen Yusuf ya kammala.
“Ku taya ni murna ga Farfesa Tajudeen Yusuf yayin da ya kammala haddace Alkur’ani mai girma. Muna alfahari da karfin zuciyarka da kaunar ka ga Littafin Allah.
"Allah ya sanya wannan ilimi ya zama hujja a gare ka, ka da ya zama hujja a kanka”
- Dr AbdulHakeem AbdulLateef
Farfesan, wanda shi ne shugaban cibiyar Masana Ilimin Kudin Harkokin Musulunci ta Najeriya (IIFP), ya dauki lokaci daga cikin jadawalin aikinsa mai cike da ayyuka domin cimma burin.
Ya bayyana damuwarsa game da rashin kyakkyawar alaka da Musulmi, musamman kwararru, ke yi da Alkur’ani, yana mai jan hankalinsu kan muhimmancin karatu da hadda.
Dan Farfesa ya kafa tarihi a jami'a
Muslim News ta ruwaito cewa labarin ya zo ne ‘yan kwanaki bayan da dansa, Abdullah Tajudeen, ya kammala digirinsa na farko a Jami’ar Legas da sakamako mai ban mamaki.
Abdullah ya samu kyakkyawan maki na CGPA 4.92, wanda ya ba shi damar zama mafi kyau a sashen Nazarin Addinin Musulunci da kuma duk fannin fasaha na jami’ar.
Abdullah, kamar mahaifinsa, shima hafizin Alkur’ani ne, wanda ya haddace Littafin Allah a cibiyar Khalwatu Tanzeel, inda ya sami horo daga malamai masu kwarewa.
Yadda Farfesa Yusuf ya yi hadda
Shi kuma Farfesa Tajudeen ya samu taimako daga wani malami na kashin kansa da ya jagorance shi mataki-mataki har zuwa kammalawa.
Wannan ya kara tabbatar da cewa haddace Alkur’ani aiki ne mai yiwuwa duk da nauyin ayyukan yau da kullum.
Farfesa Yusuf ya yi kira ga Musulmi
Farfesa Tajudeen Yusuf ya yi kira ga Musulmi masu ilimin zamani da su rika ware lokaci duk da yawan ayyukansu domin karatun Alkur’ani da haddacewa.
A taron shekara-shekara na kungiyar Guild of Muslim Professionals (GMP) da aka gudanar a Ogun, Farfesan ya nuna damuwa kan yadda wasu Musulmi ba sa ba da lokaci ga Alkur’ani.
Bikin Kur'ani ya jawo kalubale
A wani rahoton, kun ji cewa taron bikin Kur'ani da aka kira da Qur'anic Festival ya cigaba da jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya.
Wani malamin addinin Musulunci a jihar Kano, Barista Ishaq Adam Ishaq ya bukaci malamai masu goyon bayan bikin da su gabatar da dalilai.
Asali: Legit.ng