Malamin Addini Ya yi Ridda zuwa Bautar Gargajiya bayan Karatun Boko Mai Zurfi

Malamin Addini Ya yi Ridda zuwa Bautar Gargajiya bayan Karatun Boko Mai Zurfi

  • Tsohon malamin coci, Dr Echezona Obiagbaosogu, ya bayyana barinsa aikin coci domin rungumar addinin gargajiya
  • Dr Obiagbaosogu, wanda yake malami a Jami’ar Nnamdi Azikiwe, ya yi bayani ne bayan gama rubutunsa na digirin-digirgir kan maganin gargajiya
  • Malamin jami'ar ya ce manufarsa ita ce dawo da dabi’u da al’adun Afirka da suka bace a tsakanin al'umma sakamakon mulkin mallaka

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Anambra - Wani malamin cocin Katolika da ya yi shekaru 17 yana hidima, Dr Echezona Obiagbaosogu, ya sanar da ficewarsa daga aikin coci domin rungumar addinin gargajiya.

Dr Obiagbaosogu, wanda yake koyarwa a fannin Addinin Gargajiyan Afirka a Jami’ar Nnamdi Azikiwe, ya bayyana hakan ne bayan kare digirin-digirgir dinsa kan binciken sarrafa ruwan sama.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fadi alakarsa da El-Rufai, ya magantu kan barinsa APC da hana shi Minista

Fasto
Fasto ya koma bautar gargajiya. Hoto: @mfonabia6, unizik.edu.ng
Asali: Instagram

Vanguard ta wallafa cewa malamin ya ce wannan mataki ya biyo bayan burinsa na tsunduma cikin bincike da kuma dawo da dabi’un addinin gargajiya na kakanninsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin yin riddar malamin addini

Dr. Obiagbaosogu ya bayyana cewa sha’awarsa ga dabi’un kakanninsa, musamman fasahar sarrafa ruwan sama, ita ce ta ja hankalinsa ya koma addinin gargajiya.

Malamin ya ce;

“Na yi shekaru 17 a matsayin malamin coci kafin na yanke shawarar rungumar addinin gargajiya."

Dr Obiagbaosogu ya bayyana cewa wannan bincike ya biyo bayan sha’awarsa kan al’amuran dabi’ar dan Adam tare da niyyar dawo da dabi’un Afirka da suka bata cikin al'umma.

Binciken fasahar sarrafa ruwan sama

Malamin ya ce fasahar sarrafa ruwan sama na daga cikin abubuwan da suka ja hankalinsa wajen binciken al’adun gargajiya.

“Na fara sha’awar wannan fannin tun ina yaro, lokacin da nake tare da kakana wanda yake bin addinin gargajiya.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Bayan halartar taro da gwamna, kwamishina ya riga mu gidan gaskiya

Mahaifina, duk da cewa Kirista ne, yana amfani da kayan gargajiya wajen noman shi da kuma magani.”

- Dr Obiagbaosogu

Kokarin dawo dawo da darajar Afirka

Dr. Obiagbaosogu ya yi karin haske kan yadda bincikensa ya kasance wata hanya ta dawo da darajar Afirka da kuma fahimtar tasirin gargajiya a kan kimiyya.

Ya ce:

“Magani da dabarun gargajiya na Afirka na da amfani sosai wajen dawo da dabi’unmu da aka daina aiki da su.
Ban juya baya ga Allah ba, sai dai kawai ina kara fahimtar sa ta wata hanya mai ma’ana ne.”

Tribune ta wallafa cewa malamin jami'ar ya kuma zargi fina-finan Nollywood da yin amfani da al’adun gargajiya wajen bata sunan Afirka.

Dr Obiagbaosogu ya ce ya samu nasara

Dangane da shawarar barin aikin coci, Obiagbaosogu ya bayyana hakan a matsayin wani bangare na ci gaban rayuwa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ware biliyoyin Naira kan jiragen shugaban kasa a 2025

Ya bayyana cewa rayuwa wani tsari ne, saboda haka mutum ya kamata ya fahimci kansa da kuma abin da ya dace da rayuwarsa.

A cewarsa, wannan mataki yana da nasaba da gano kansa da kuma karuwar fahimtarsa kan dabi’un Afirka da tasirin su ga al’umma.

Tsohon malamin ya yi kira ga al’ummar Afirka da su rungumi dabi’unsu domin dawo da martabarsu a duniya.

An kashe 'ya'yan boka 3 a Anambra

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan bindiga sun kai hari gidan wani boka inda suka yi masa ta'addanci.

Rahotanni sun nuna cewa 'yan bindigar sun kashe 'ya'yan bokan uku kuma sun jefa su a cikin wata motar da aka ajiye a farfajiyar gidansa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng