Kwankwaso Ya Jero Mutane Ya Musu Godiya bayan Auren Yarsa

Kwankwaso Ya Jero Mutane Ya Musu Godiya bayan Auren Yarsa

  • Jagoran NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi magana karon farko bayan daura auren yarsa, Dr Aisha da Fahad Dahiru Mangal
  • Rabi'u Musa Kwankwaso ya mika godiya ga dukkan mutanen da suka taho Kano daga jihohi suka taya shi murnar bikin yarsa
  • An daura auren Aisha Rabi'u Musa Kwankwaso da Fahad Dahiru Mangal ne a fadar mai martaba Muhammadu Sanusi II

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Bayan daurin auren yarsa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya mika godiya ga al'umma.

A yau Asabar, 16 ga Nuwamba Nuwamba aka daura auren Aisha Kwankwaso da Fahad Dahiru Mangal inda manyan mutane suka shaida bikin.

Yar Kwankwaso
Kwankwaso ya yi godiya ga wadanda suka shaida auren yarsa. Hoto: Saifullah Hassan
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro jawabin godiya da Rabi'u Kwankwaso ya tura ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Manyan Najeriya da suka hallara auren yar Kwankwaso da dan Mangal a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso ya yi godiya ga al'umma

Sanata Rabi'u Kwankwaso ya godewa shugaba Bola Tinubu da ya tura Kashim Shettima ya wakilce shi wajen daurin auren.

Haka zalika ya yi godiya ga Olusegun Obasanjo, Atiku Abubakar, kakakin majalisar dattawa, Hon. Abbas Tajudeen.

Kwankwaso ya godewa Abba Kabir Yusuf, mataimakin gwamnan Kano da sauran jami'an gwamnatin jihar bisa gudunmawar da suka bayar yayin bikin.

"Ina godiya da sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II a kan karrama bakina da ya yi a fadarsa. Ina godewa sarakunan Gaya, Rano da Karaye.
Ina godiya ga dukkan gwamnoni da ke kan karaga da tsofaffi, ministoci, yan majalisu, malaman addini da sauransu."

- Sanata Rabi'u Kwankwaso

Madugun Kwankwasiyya ya godewa mutanen jihar Kano bisa hadin kai da suka bayar wajen tafiyar auren yadda ya kamata.

A karshe, Rabi'u Kwankwaso ya yi addu'ar Allah ya mayar da kowa gidansa lafiya musamman wadanda suka taho daga nesa.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya zama waliyyin ango, an bayyana sadakin diyar Kwankwaso

Mutane sun shaida auren yar Kwankwaso

A wani rahoton, kun ji cewa manyan mutane a ciki da wajen Najeriya sun halarci bikin auren yar Kwankwaso.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, Olusegun Obasanjo, Atiku Abubakar na cikin manyan mutanen da suka shaida auren.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng