Manyan Najeriya da Suka Hallara Auren Yar Kwankwaso da Ɗan Mangal a Kano

Manyan Najeriya da Suka Hallara Auren Yar Kwankwaso da Ɗan Mangal a Kano

A ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba aka daura auren Dr Aisha Rabi'u Kwankwaso da Fahad Dahiru Mangal a jihar Kano.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - An daura auren Dr Aisha Rabi'u Kwankwaso da Fahad Dahiru Mangal a fadar mai martaba Muhammadu Sanusi II.

Manyan mutane, yan siyasa da yan kasuwa a ciki da wajen Najeriya sun halarci daurin auren a yau Asabar.

Yar Kwankwaso
Manyan mutane da suka shaida auren yar Kwankwaso. Hoto: Saifullahi Hassan
Asali: Facebook

A wannan rahoton, mun tattaro muku jerin jiga jigan mutane 10 a fadin Najeriya da suka halarci daurin auren.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Sanata Kashim Shettima

Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya halarci daurin auren yar Kwankwaso.

Legit ta wallafa cewa Sanata Kashim Shettima ne ya karbawa Fahad Dahiru Mangal auren Dr Aisha.

2. Olusegun Obasanjo

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Bayan T Pain, Obasanjo ya raɗawa Tinubu sabon suna

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo na cikin manyan Najeriya da suka halarci auren.

A cikin wata shiga ta ban mamaki, Olusegun Obasanjo ya saka jar hula da take nuna mubaya'a ga darikar Kwankwasiyya.

3. Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya shaida daurin auren Aisha Rabi'u Kwankwaso.

Atiku Abubakar ya wallafa a shafinsa na Facebook yayin da ya isa jihar Kano a safiyar yau Asabar.

4. Bukola Saraki

Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Abubakar Bukola Saraki ma ya ziyarci jihar Kano domin shaida auren Fahad da Aisha.

5. Sheikh Abdullahi Bala Lau

Shugaban kungiyar Izala na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya isa Kano shaida auren Aisha Kwankwaso tun ranar Juma'a.

6. Sheikh Muhammad Kabiru

Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe ya kasance cikin malaman da suka yi wa'azi yayin liyafar auren Aisha Kwankwaso.

7. Abdulaziz Yari

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari na cikin manyan mutane da suka isa Kano domin taya Kwankwaso murnar auren yarsa.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya zama waliyyin ango, an bayyana sadakin diyar Kwankwaso

8. Abbas Tajudeen

Kakakin majalisar dokokin Najeriya, Hon. Abbas Tajudeen na cikin manyan yan siyasa da suka shaida auren.

9. Aminu Waziri Tambuwal

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya shiga sahun manyan mutane da suka halarci daurin auren Fahad Dahiru Mangal a Kano.

10. Dikko Umaru Radda

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya hallara daurin auren yar Kwankwaso bayan dawowa daga Amurka.

Manyan baki a bikin Kwankwaso-Mangal

Sauran wadanda suka halarci bikin ko suka iso Kano kafin ranar daurin auren sun hada da Ahmad Makarfi da Adamu Aliero.

An ga tsofaffin gwamnonin jihohin Edo, Bauchi, Kwara, Akwa Ibom da sauransu.

Muhammad Badaru Abubakar da Ahmad Dangiwa wadanda ministoci ne a gwamnatin Bola Tinubu sun halarci bikin.

Legit Hausa ta hangi Hamza Al-Mustapha, Lado Danmarke, Ali Ndume da manyan da ke rike da mukamai a jam'iyyar NNPP a Najeriya.

An yi liyafar auren Aisha Kwankwaso

A wani rahoton, kun ji cewa an gudanar da liyafar yar Kwankwaso a jiya Juma'a 15 ga watan Nuwambar 2024 wanda ya samu halartar Sheikh Kabiru Gombe.

Hakan ya jawo ce-ce-ku-ce daga wasu yan Najeriya da suke ganin bai dace malamai su halarci wurin da ke da maza da mata ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng