Yar Buhari, Fatima Ta Zamo Jakadar ANAN Ta Farko a Najeriya
- Kungiyar ANAN ta naɗa yar tsohon shugaban kasa, Fatima Muhammadu Buhari a matsayin Jakada ta farko a Najeriya
- Lamarin ya biyo bayan zabe da rantsar da Fatima Buhari a matsayin shugabar kungiyar mata ta PROWAN a jihar Katsina
- Shugaban kungiyar ANAN na kasa, James Neminebor ya bukaci dukkan yan kungiyar su yi aiki tare wajen kawo cigaba a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina - An yi taro na musamman domin nada yar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari Jakada.
Kungiyar akantoti ta kasa, ANAN ta nada Fatima Muhammadu Buhari a matsayin Jakada ta farko a Najeriya.
Jaridar Leadership ta wallafa cewa gwamna Dikko Umaru Radda ya ce zai ba kungiyar hadin kai yadda ya kamata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
ANAN ta nada Fatima Buhari Jakada
Kungiyar ANAN ta nada yar tsohon shugaban kasa, Fatima Muhammadu Buhari matsayin Jakada ta farko a Najeriya.
Haka zalika an rantsar da Fatima Buhari a matsayin shugabar kungiyar mata akantoti ta jihar Katsina, PROWAN.
Yar tsohon shugaban kasar ta tabbatar da cewa za ta yi kokari wajen kawo cigaba bisa karramata da matsayin da aka yi.
"Matsayin da aka ba ni yana nuna irin gwagwarmayar da mata ke yi a yankin Arewa ta Yamma da ma Najeriya baki daya.
Za mu yi aiki domin ɗaga darajar mata wajen ba su ilimi mai inganci da za su zamo abin kwatance."
- Fatima Muhammadu Buhari
Shugaban kungiyar ANAN na Najeriya, James Neminebor ya bukaci yan kungiyar da su kasance jakadu na gari a duk inda suke.
Mataimakin gwamnan Katsina, Faruk Jobe da ya wakilci gwamna Dikko Umaru Radda a taron ya ce gwamnatin jihar za ta hada kai da ANAN domin cigaba.
Yar Tinubu ta zamo Jakadar almajirai
A wani rahoton, kun ji cewa ma'aikatar lura da almajirai da yaran da ba su zuwa makaranta ta ba yar Bola Ahmed Tinubu matsayin jakada.
Shugaban ma'aikatar, Muhammad Sani Idris ne ya bayyana lamarin a wata ziyara da ya kai wa yar shugaban kasar a jihar Legas.
Asali: Legit.ng