‘Diyar Shugaban Najeriya, Fatima Buhari ta samu babbar kujera a Majalisar CIFCFEN

‘Diyar Shugaban Najeriya, Fatima Buhari ta samu babbar kujera a Majalisar CIFCFEN

  • Fatima Muhammadu Buhari ta samu shiga cikin majalisar amintattun CIFCFEN
  • An yi bikin rantsar da Fatima Buhari da wasu mutane 17 a birnin tarayya Abuja
  • Shugaban cibiyar, Iliyasu Gashinbaki, ya yaba da kwarewar ‘Yar shugabar kasar

Abuja - Hajiya Fatima Muhammadu Buhari ta samu mukami a majalisar CIFCFEN ta Najeriya.

Jaridar The Cable ta fitar da rahoto cewa Fatima Muhammadu Buhari ta samu matsayi a cibiyar da ke koyar da bincike da bankado masu sata.

Kungiyar akawun nan na kasa watau ANAN ce ta kafa wannan cibiyar ta CIFCFEN domin a yaki satar kudi da ta jarrabawa da ake yi a Najeriya.

An yi bikin wannan nadi da sauran mutane 17 a babban ofishin CIFCFEN da ke ANAN House a unguwar Mabushi, babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Hotunan Osinbajo na gudu a filin motsa jiki yayin karbar bakuncin gasar Baton

Fatima Muhammadu Buhari ta na cikin ‘ya ‘yan shugaban Najeriya mai-ci Muhammadu Buhari. An haife ta ne a watan Maris a shekarar 1975.

Iyalan Buhari
Wasu 'Ya 'yan Shugaban kasa Buhari Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meyasa aka zabi Fatima Buhari?

Da yake magana wajen bikin, shugaban CIFCFEN Dr. Iliyasu Gashinbaki yace Fatima Muhammadu Buhari ta shigo cibiyar da dinbin ilmi.

Iliyasu Gashinbaki yace Buhari za ta taimaka wa cibiyar domin ta san aiki, kuma tana da kware wa sosai, sannan akwai bukatar a rika tafiya da mata.

A jawabinta, Hajiya Fatima Buhari ta yi godiya da makarantar ta zabe ta, har ta amince ta ba ta wannan babban mukami a majalisar amintattunta.

Hajiya Fatima Muhammadu Buhari

Fatima ta yi digirin farko a ilmin akawu a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Bayan nan ta karo karatu a ilmin akawu da tattali a jami’ar Stratford.

Wannan Baiwar Allah tayi digirin Masters a bangaren kasuwanci a jami’arAnglia Ruskin. Bayan haka tana da wani digirin a jami’ar Northampton.

Kara karanta wannan

Jerin wasu nasarori 12 da Buhari ya cimma a shekaru 2, wa'adin mulkinsa na biyu

Ba a nan ta tsaya ba, Fatima ta samu shaidar PGD har ila yau a wata jami’a duk a Birtaniya. Yanzu haka tana yin digirinta na PhD a harkar kasuwanci.

#PandoraPapers

A makon nan aka ji binciken Pandora Papers ya nuna akwai attajirai da ‘Yan kasuwan Najeriya da suka tara kudi da kadarorin a kasashen ketare.

Wasu suna yin dabarar tara dukiya, ana juya wa ba tare da hukumomi sun sani ba. Hakan ya sa wadannan mutane suka tara dukiya mai yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng