'An Fatattake Ni daga Fada' An yi wa Shahararren Sarki a Najeriya Wulakanci

'An Fatattake Ni daga Fada' An yi wa Shahararren Sarki a Najeriya Wulakanci

  • Mai Martaba Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi ya fadi wasu abubuwan da suka faru tsakanin shi da wani sarki
  • Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi ya ce wata rana ya ziyarci fadar Oluwo na Iwo Oba Abdulrasheed Akanbi amma abin bai yi kyau ba
  • An ruwaito cewa Oba na Iwo, Abdulrasheed Akanbi ya saba da gardagi ga masu bautar gumaka a Osun da ma kasar Yarabawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Osun - Mai martaba Ooni na Ife ya bayar da labarin yadda aka fatattake shi yayin wata ziyara.

Ooni na Ife ya bayyana cewa lamarin ya faru ne yayin da ya ziyarci Oba na Iwo, Oba Abdulrasheed Akanbi a fadarsa.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya fadi kokarin da ya yi da yake mulki, ya koka da rashin tsaro a yau

Ooni na Ife
An fatattaki Ooni na Ife a fadar Iwo. Hoto: @ooniadimulaife, @king_oluwo
Asali: Instagram

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Oba Abdulrasheed Akanbi yana kira ga al'umma kan kaucewa bautar gumaka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka fatattaki sarki daga fada

Leadership ta wallafa cewa Ooni na Ife ya labarta cewa watarana Oba na Iwo Abdulrasheed Akanbi ya fatattake shi.

Oba Adeyeye Enitan ya bayyana cewa an masa kora kamar karamin yaro a lokacin da ya ziyarci sarkin a fadarsa.

Ooni na Ife ya nisanci Oba na Iwo

A yayin da aka bukaci Ooni na Ife ya kai ziyara wa Oba na Iwo ya ce ba zai kara zuwa wajensa ba. Ga abin da ya ce:

"Tun a lokacin da ya kore ni kamar karamin yaro na nisance shi.
A yanzu ku da kuke cewa na kai masa ziyara, me za ku ce idan ya mani abin da yake so na wulakanci?

Kara karanta wannan

'Sai an kula kashi': Atiku ya yi wa ministan Tinubu, Wike wankin babban bargo

Amma duk da haka zan cigaba da girmama shi a matsayinsa na babban mutum mai daraja"

Maganar Sarkin Iwo kan bautar gumaka

An ruwaito cewa Oba Abdulrasheed Akanbi ya saba kira ga al'umma a kan nisantar bautar gumaka.

Ya kuma gargadi mutane cewa ba zai yarda da bautar gumaka a Iwo ba kuma duk wanda ya yi zai dandana kudar shi.

Sarki Sanusi II ya ziyarci jihar Jigawa

A wani rahoton, kun ji cewa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya kai ziyara jihar Jigawa bayan mummunan hadarin tankar man fetur.

Sarki Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa a wannan lokacin ne ya fara zuwa fadar gwamnatin jihar Jigawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng