Naci da Kokari: ’Yar Shekaru 19 Ta Sace Zukatan Mutane Bayan Kammala Digiri da Makin 5.0 GPA
- Wata matashiya ‘yar Najeriya ta kafa tarihi a jami’ar Babcock, Ilishan-Remo bayan kamala digiri dinta
- Dalibar ta kamala digirin farko a kimiyyar na’ura mai kwakwalwa tare da samun makin 5.0 GPA a shekarar karshe
- Matashiyar mai shekaru 19 ta kai batun kafar sada zumunta, inda ta bayyana murna da farin cikin kamala karatunta, ta nuna lambobin yabon da aka ba ta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Solarin Seun Sarah, wata matashiya ‘yar Najeriya ta kammala digirinta da maki mafi yawa a fannin kimiyyar na’ura mai kwakwalwa a jami’ar Babcock.
A wani rubutun da ta yada a kafar X (Twitter) a ranar 18 ga watan Oktoba, Sarah ta sanar da irin nasarar da ta samu tare da yada hotunan yaye ta daga jami’a.
Hakazalika, Sarah ta hada da wani rubutun da ta yi a shafinta na LinkedIn, inda ta bayyana kammala karatun na ta a fitacciyar jami’ar ta Kiristoci a ranar 28 ga watan Yuli.
Yadda ta yada labarinta
A rubutun na LinkedIn, Sarah ta ce an karrama ta da lambar yabon dalibar da ta fi kowa kwazo a tsangayar kimiyyar na’ura mai kwakwalwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakazalika, ita ce daliba mafi samun maki mai yawa a shekarar, inda ta kammala da maki 5.0 GPA na ma’aunin jami’ar.
An ba ta lambobin yabo daban-daban don taya ta murna da kuma karfafa kwazonta. Daliba ce mai shekaru 19 kacal.
Ta kuma bayyana godiyarta ga ubangiji da ya ba ta damar samun wannan babbar nasara ta rayuwa.
Jama’a sun taya Sarah murna
Legit ta tattaro kadan daga abin da jama’a ke cewa a kafafen sada zumunta bayan da Sarah ta yada abin da ya faru da ita na farin ciki, ga kadan daga ciki:
@Directorpizzy:
“Ina taya ki murna... sama, sama, kin ji.
“Makarantu masu lyau ba za su kaskanta ba. Lambar yabo ga daliba mafi kwazo, a wasu makarantun shan hannu ne kawai da VC da kuma wasu manya..ki ci gaba da kokari. Ina taya ki murna.”
@Princeola82:
“Wannan lamari ne mai girma kuma abin sha’awa. Alama ce ta ci gaba. Ina taya ki murna. Ina jinjina miki. Akwai mutane da masu hazaka da girma a manhajar X.”
@veephilemon:
“Babbar magana!!!!! Ina taya ki murna yarinya!!!! Kin yi komai!!!!!”
@opening_petals:
“Ina taya ki murnar wannan babban al’amari!!! 🎉🎉🎉 Allah ya kara daukaka.”
@D_GlobalActuary:
“Ina taya ki murna🎉, wannan mafarin nasarori da sunan Yesu.”
@yourpman:
“Kwazo ya hadu da naci 👏 ina taya ki murna.”
@certnsmbdy74:
“Ina taya ki murna!!!! Ina matukar alfahari da ke!”
'Yar Arewa ta kafa tarihi
A wani labarin, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya uwargidan tsohon gwamnan jihar Kebbi murna kan tarihi da ta kafa a nahiyar Afirka.
A ranar 8 ga watan Oktoba aka zabi Dr Zainab Shinkafi Bagudu ta shugabanci kungiyar UICC a fadin duniya.
Hadimin shugaban kasa a harkar sadarwa, Bayo Onanuga ne ya wallafa sakon taya murnar a shafinsa na X.
Asali: Legit.ng