'Sai Mun Hadu a Aljanna ', Shugaban NNPCL, Kyari Ya Magantu kan Rasuwar Yarsa

'Sai Mun Hadu a Aljanna ', Shugaban NNPCL, Kyari Ya Magantu kan Rasuwar Yarsa

  • Kwana biyu da rasuwar Fatima Kyari, mahaifinta, Mele Kyari ya yi maganar rashinta, ya nuna alhinisa da yi mata addu'a
  • Kyari ya mika godiya ta musamman ga shugabanni da al'umma da sauran yan uwa kan addu'o'i da suka yi ta yi
  • Shugaban kamfanin NNPCL ya yi addu'ar Ubangiji ya yi mata rahama, ya ce suna fatan haduwa a gidan aljanna a kiyamas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari ya yi magana kan rashin yarsa da ya yi a ranar Juma'a.

Mele Kyari ya yi godiya ga al'ummar Najeriya kan addu'o'i da addu'o'i da kuma alhini da suka masa yayin rashin.

Kara karanta wannan

'Ba yan ta'adda ba ne', Sarkin Zazzau ya fadi yadda Fulani suke, ya kawo dalili

Mele Kyari ya godewa al'umma kan addu'o'in da suka yi na rashin yarsa
Shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari ya yi alhinin rasuwar yarsa. Hoto: @MKKyari.
Asali: Twitter

Mele Kyari ya yi jimamin rasuwar yarsa

Shugaban kamfanin ya bayyana haka a yau Talata 15 ga watan Oktoban 2024 a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kyari ya yi jimamin rasuwar yar tasa, ya ce ta bar duniya a lokacin da ya dace.

"Yata, Fatima ta rasu a lokacinta, ina fatan mu hadu da ita a gidan Aljanna Firdausi da yardar Allah."
"Duk da akwai daci rashinta, amma mun godewa Allah da dukkan ni'imominsa."
"Ina godiya ga shugabanni da yan uwa da abokan arziki kan taya mu alhini game da rashinta."

- Mele Kyari

Kyari ya fadi yadda Fatima ta taimaki al'umma

Kyari ya ce marigayiyar ta taba rayuwar al'umma da dama duk da matsalar da take da shi na halitta a zahiri.

Shugaban kamfanin NNPCL ya bayyana yadda rashin Fatima ya hada kan mutane gaba daya wanda ke nuna tausayi.

Kara karanta wannan

Kanin tsohon gwamna ya ayyana kansa shugaban PDP, ya kori Atiku, Wike da sauransu

Shettima ya yi jajen rasuwar yar Kyari

Kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya samu halartar jana'izar yar shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari.

Kashim ya yi jimamin rasuwar Fatima Kyari mai shekaru 25, ya yi addu'ar Ubangiji ya yi mata rahama ya sa ta gidan aljanna.

Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayiyar Fatima ta rasu a ranar Juma'a 11 ga watan Oktoban 2024 a birnin Tarayya Abuja bayan fama da jinya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.