Shugaban Izala, Sheikh Bala Lau Ya yi Babban Rashi, za a yi Janaza a Adamawa

Shugaban Izala, Sheikh Bala Lau Ya yi Babban Rashi, za a yi Janaza a Adamawa

  • Shugaban kungiyar Izala na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yi babban rashi a safiyar yau Talata, 8 ga watan Oktoba
  • Sheikh Abdullahi Bala Lau ya rasa daya daga cikin surukarsa mai suna Hajiya Zainab a Jimeta da ke jihar Adamawa
  • Rahotanni sun nuna shirye shiryen yi wa Hajiya Zainab janaza sun kammala kuma an saka lokaci da wajen jana'izarta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Adamawa - Rahotanni da suka fito daga Adamawa na nuni da cewa shugaban Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yi babban rashi.

An ruwaito cewa surukar Sheikh Abdullahi Bala Lau ce Allah SWT ya yi wa rasuwa a yau Talata a jihar Adamawa.

Kara karanta wannan

Carbi: Za a buga muƙabala mai zafi tsakanin Pantami da Idris Dutsen Tanshi

Sheikh Bala Lau
Surukar Sheikh Bala Lau ta rasu. Hoto: Jibwis Nigeria
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan rasuwar Hajiya Zainab ne a cikin wani sako da shafin Jibwis Najeriya ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Surukar Sheikh Abdullahi Bala Lau ta rasu

A yau Talata aka samu rahotonni kan rasuwar surukar shugaban kungiyar Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau.

Hajiya Zainab da aka fi sani da Hajja Diya ta rasu ne a jihar Adamawa kamar yadda rahotanni suka nuna.

Wata majiya ta tabbatarwa Legit cewa marigayiya Hajja Diya ita ce mahaifiyar uwargidar shugaban na Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau.

Yaushe za a yi janazar surukar Sheikh Bala Lau?

Bayan rasuwar Hajja Diya, an ruwaito cewa za a mata janaza ne a yau Talata da misalin karfe 1:20 na rana.

Haka zalika sallar janazar za ta kasance ne a masallacin Jumu'a na Doubeli da ke karamar hukumar Jimeta a jihar Adamawa.

Kara karanta wannan

'Ba za mu ba Tinubu takara ba,' Jigon APC ya tono wani shiri kan zaben 2027

Tuni dai al'ummar musulmi suka rika tururuwan yi wa Hajiya Zainab addu'ar samun rahama da kuma tura sakon jaje ga shugaba Sheikh Abdullahi Bala Lau.

Shugaban Izala a jihar Kebbi ya rasu

A wani rahoton, kun ji cewa a makon da ya wuce kungiyar Izalar Jos da Sheikh Sani Yahaya Jingir ke jagoranta ta sanar da rasuwar shugaban gudanarwanta.

Rahotanni da suka fito sun nuna cewa Sheikh Shua'ibu Muhammad Sarkin Fawa ya rasu ne bayan jinya a gadon asibiti a jihar Sokoto.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng