An Fatattaki Mutumi a Masallacin Abuja bayan Ya Zo Musulunta, An Gano Makircinsa

An Fatattaki Mutumi a Masallacin Abuja bayan Ya Zo Musulunta, An Gano Makircinsa

  • Wani mutumi ya shiga matsala a masallacin Abuja bayan korarsa da aka yayin da ya zo Musulunta a yau Juma'a
  • An fatattaki mutumin ne kan zargin yaudara da kuma damfara inda yake zuwa coci da masallatai da sunan sauya addini
  • Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani shi ya bayyana haka a yau Juma'a 4 ga watan Oktoban 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - An gano wani shiri da wani ke yi na damfarar al'umma a masallatai da coci a Abuja.

Sanata Shehu Sani ya ce an fatattaki mutumin ne bayan ya zo masallaci a matsayin wanda ya Musulunta.

An fitar da wani mutum a masallacin Abuja bayan ya zo Musulunta
Musulmai a masallacin Abuja sun fatattaki wani mutum a masallacin bayan ya zo Musulunta kan zargin damfara. Hoto: Legit.
Asali: Original

Mai canza addinin karya a masallacin Abuja

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun fatattaki masu sallar juma'a a wasu masallatai a Katsina

Shehu Sani ya bayyana haka ne a yammacin yau Juma'a 4 ga watan Oktoban 2024 a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanatan ya ce an gano yadda mutumin ya ke karyar Musulunta da kuma komawa Kiristanci a coci domin damfarar al'umma.

Tsohon sanatan ya ce tuni aka kori mutumin daga cikin masallacin Abuja domin dakile damfarar al'umma da yake yi.

"An fatattaki wani mutum a masallacin Abuja a yau Juma'a 4 ga watan Oktoban 2024."
"An yi hakan ne saboda gano yadda yake komawa Musulunci da Kiristanci a coci da masallatai domin samun kyaututtuka daga mutane."

- Shehu Sani

Martanin wasu kan abin da ya faru a Abuja

Wasu yan Najeriya sun fadi albarkacin bakinsu game da abin da ya faru a masallacin da aka ce yake a birnin Abuja.

@EvangelinChinyere:

"Ya kamata a kai shi kotu, bai kamata a sake shi ba, wannan ba abin wasa ba ne, ta haka muke zaben gurbatattun shugabanni."

Kara karanta wannan

Bayan kashe Halilu Sububu, hafsan tsaro ya fadi halin da Bello Turji yake ciki yanzu

@bizwina:

"Yunwa zai saka tunani sosai lallai."

@flourish007:

"Wannan kaman yan siyasa daga APC, Tinubu ya sauya sheka, Atiku ya yi, Peter Obi ya yi shi ma."

An shawarci Tinubu ya ba Shehu Sani Minista

Kun ji cewa an buƙaci Bola Tinubu da ya naɗa Nasir El-Rufai a matsayin minista a yayin da yake shirin yin garambawul a majalisar FEC.

Ƙungiyar Mandate Protection Vanguard (MPV) ta ba da wannan shawarar ne a cikin wata sanarwa da shugabanta ya fitar.

A cewar ƙungiyar, Shehu Sani da wasu mutane uku ya kamata a ba su muƙamai domin su yi wa ƙasa hidima ƙarƙashin Tinubu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.