‘Za Mu Fitar da Tauraro a Kowane Gida,’ Kwankwaso Ya yi Albishir ga Talakawa

‘Za Mu Fitar da Tauraro a Kowane Gida,’ Kwankwaso Ya yi Albishir ga Talakawa

  • Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana babban burinsa a kan talakawan Najeriya
  • Sanata Rabi'u Kwankwaso ya bayyana cewa ya kamata kowane dan siyasa mai kishi ya taimakawa al'umma a kawo cigaba
  • Jagoran NNPP na kasa ya ce yanna fatan yan Najeriya su waye da siyasar akida ta yadda ba za su zabi wanda bai dace ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano kuma babban 'dan siyasa, Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi albishir ga talakawa.

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce babban burinsa shi ne taimakawa talakawa, ya fitar da su daga wahalar rayuwa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi ta'aziyyar yan maulidi 150 da ake fargabar sun mutu a hadarin jirgi

Kwankwaso
Kwankwaso ya yi albishir ga talakawa. Hoto: Rabi'u Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Kwankwaso ya fadi haka ne cikin wata hira da ya yi kamar yadda hadiminsa, Saifullahi Hassan ya wallafa bidiyon a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganar fitar da tauraro a gidan talaka

Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce idan tafiyar NNPP da Kwankwasiyya suka yi karfi talakawa za su amfana.

Kwankwaso ya ce za su rika zakulo mutane a gidajen talakawa futuk suna ba su ilimi domin su zama taurari a rayuwarsu kuma su taimaki al'umma.

Tsohon gwamnan ya ce sun yi irin haka a baya kuma yanzu haka mutanen da suka taimakawa sun zama abin kwatance a duniya.

Rabiu Kwankwaso ya bukaci gyara tsarin siyasa

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce akwai bukatar mutane su waye su rika siyasar akida wajen zaben wadanda suka cancanta.

Kwankwaso ya kara da cewa bai kamata mutane suna karbar taliya suna zaben yan siyasa da ba su tausayin talaka ba.

Kara karanta wannan

'Ya lalata komai,' Kwankwaso ya tono 'barnar' da Ganduje ya yi a Kano

Ya kara da cewa irin yan siyasar burinsu shi ne kawai su rika danne talakawa a kullum kuma taliyar da suke rabawa ma daga cikin dukiyar talaka ne.

Kwankwaso ya ce an lalata ilimi a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamna Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi hira da manema labarai kan harkar ilimi a jiya da yau a Kano.

Sanata Rabi'u Kwankwaso ya zargi tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje da lalata harkokin ilimi a jihar a shekaru takwas.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng