Akwa Ibom: Muhimman Abubuwa 5 kan Matar Gwamna da Ta Rasu
- A yau Juma'a hukumomi suka sanar da rasuwar matar gwamnan jihar Akwa Ibom, Patience Umo Eno.
- An ruwaito cewa Patience ta rasu ne bayan wata jinya da ta yi a wani asibiti duk da ba a fadi me ke damunta ba
- A wannan rahoton, mun tattaro muku wasu muhimman abubuwa da suka shafi rayuwar Patience Umo Eno
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Akwa Ibom - Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta tabbatar da rasuwar matar gwamna Umo Eno mai suna Patience Eno.
Kwamishinan yada labaran gwamnatin jihar, Ini Emembong ne ya fitar da sanarwar mutuwar inda ya ce ta rasu ne bayan gajeruwar jinya.
A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku wasu muhimman abubuwa da suka shafi rayuwar Patience Eno.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abubuwan 5 kan matar gwamnan da ta rasu
1. Matar gwamna ta rasu ta na shekaru 57
Jaridar the Nation ta wallafa cewa a watan Fabrairu da ya wuce Patience Eno ta cika shekaru 57 kuma ta yi wani gagarumin taro.
An ruwaito cewa a yayin bikin, ta raba kyautar kudi da wasu abubuwa masu muhimmanci ga mabukata.
2. Marigayiya ta fito daga Ikot Akpa Ekop
Bincike ya nuna cewa Patience Eno yar asalin yankin Ikot Akpa Ekop ne a jihar Akwa Ibom, kuma ta girma ne a cikin garin Akwa Ibom.
3. Malamar addini ce
An ruwaito cewa Patience Eno ta kasance daya daga cikin fastoci masu koyar da addinin Kirista a jihar Akwa Ibom.
4. Tana da 'ya'ya 6
Rahotanni sun nuna cewa matar gwamnan ta haifi 'ya'ya shida kafin rasuwarta kuma tana da jikoki tara.
5. Shekaru 37 da auren gwamna
Bayanai sun nuna cewa matar gwamnan jihar Akwa Ibom ta yi shekaru sama da 37 tana zaman aure a gidan miji.
Rasuwar matar gwamna ya tsaida yakin zabe
A wani rahoton, kun ji cewa mutuwar mai dakin mai girma gwamnan jihar Akwa Ibom, Patience Eno ta jefa jihar cikin alhini da takaici.
A sakon ta'aziyyarta ga gwamna Umo Eno, PDP a jihar ta yi addu'ar samun dangana ga iyalan marigayiyar.
Jami'in hulda da jama'a na PDP a Akwa Ibom, Edwin Ebiese ya sanar da dakatar da yakin neman zaben da ake yi a jihar a halin yanzu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng