Jonathan Ya Ci Gyaran Sanusi II, Ya Fadi Dalilin Dakatar da Shi a CBN a 2014

Jonathan Ya Ci Gyaran Sanusi II, Ya Fadi Dalilin Dakatar da Shi a CBN a 2014

  • Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi magana kan dakatar da Muhammadu Sanusi II daga gwamnan babban banki
  • Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi ya yi zargin cewa Jonathan ya dakatar da shi ne saboda ya fallasa badakalar kudi a gwamnatinsa
  • Sai dai a yayin wani taro a Abuja, Dr. Goodluck Jonathan ya wanke kansa daga zargin kuma ya fadi dalilin dakatar da gwamnan a 2014

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi magana kan sauke sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II daga gwamnan CBN.

Shugaba Jonathan ya ce akwai kuskure cikin bayanin da Sanusi II ya yi kan dalilin sauke shi daga gwamnan Bankin CBN.

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya yiwa Jonathan martani kan tsige shi daga gwamnan CBN a 2013

Jonathan
Jonathan ya fadi dalilin sauke Sanusi II daga CBN. Hoto: Goodluck Ebele Jonathan|Masarautar Kano
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa shugaba Jonathan ya hadu da Sanusi II ne a wani taro a birnin tarayya Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A CBN, Sanusi ya yi zargin batan $49.8bn

A lokacin mulkin shugaba Goodluck Jonathan, Sanusi II ya yi zargin cewa makudan kudi har $48.9b sun bata.

Sarki Muhammadu Sanusi ya yi zargin cewa shugaba Jonathan ya sauke shi ne bisa dalilin bankaɗo badakalar.

'Dalilin dakatar da Sanusi a CBN' - Jonathan

Goodluck Jonathan ya ce sam ba maganar batan $49.8b ba ce ta saka ya dakatar da Sanusi II daga gwamnan CBN.

Jonathan ya bayyana cewa ya samu korafi ne daga kwamitin FRC mai lura da yadda ake kashe kudin gwamnati kan cewa CBN ya kashe makudan kudi.

Ashe Jonathan ya yi niyyar dawo da Sanusi II?

Shugaba Goodluck Jonathan ya ce bayan kammala bincike ya yi niyyar dawo da Sanusi II CBN amma sai aka samu akasi wa'adinsa ya kare.

Kara karanta wannan

Zargin $49bn: Jonathan ya maidawa Sanusi II martani kan satar kudi a gwamnatinsa

Rahoton Channels Television ya nuna cewa Jonathan ya ce bai son yawan surutu kan lamarin kasancewar yanzu haka sarki Sanusi ya dawo uban kasa a Najeriya.

Tsohon shugaba Jonathan ya yi magana kan zabe

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan ya yi magana kan zaben gwamna da ya gabata a jihar Edo ranar Asabar.

Shugaba Goodluck Jonathan ya bayyana cewa amfani da kimiyya da fasaha kawai ba za ta magance matsalolin maguɗin a zabe ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng