Gaskiya Ta Yi Rana: Matukin Adaidaita Sahu Ya Samu Tukwici kan Kudin Tsintuwa

Gaskiya Ta Yi Rana: Matukin Adaidaita Sahu Ya Samu Tukwici kan Kudin Tsintuwa

  • Wani matashi Bashir Muhammad ya nuna halin kwarai bayan mayar da wasu kaya da aka manta a baburinsa
  • Wasu matasa da ke halartar taron kasa da kasa a jami'ar Bayero ne su ka manta kayan a cikin adaidaita sahunsa
  • Kwana guda bayan manta kayan, Bashir Muhammad ya mayar da su zuwa jami'ar Bayero a Kano inda ya burge jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Wani matukin baburin adaidata sahu, Bashir Muhammad ya samu kyaututtuka bayan ya mayar da kayan da aka manta a baburinsa.

Matashin da aka fi sani da Bashir Itata ya dauko fasinjoji daga Jami’ar Bayero inda su ka halarci taron kasa-kasa zuwa tashar mota a gaba da Hotoro.

Kara karanta wannan

"Sai an sake zama:" Sanatan APC ya nemi Tinubu ya kira taron gaggawa kan tattali

Jihar
An yi kyautar kudi da dan adaidaita sahu Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa amma sai aka samu akasi fasinjojin su ka yi mantuwar kayayyaki masu matukar amfani a abin hawan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Direba ya maida kayan tsintuwa a Kano

Washegarin ranar da aka manta kaya a adaidata sahunsa ne, Bashir ya mayar da kayan Jami’ar Bayero inda ya dauko fasinjojin.

Daga nan sai ya mika kayan dakin taron da ke gudanar, inda aka yi shela domin masu kayan su zo su karbi abin su.

An yaba da gaskiyar mai adaidata sahu

Sani Bala, daya daga cikin wanda su ka manta kayansu a adaidata sahun Bashir, ya ce gaskiyar matashin ta yi wa jama’ar taron dadi.

A nan ne mahalarta taron su ka rika miko masa kyaututtuka har aka tattaro masa N600,000, lamarin nan ya yi wa jama’a dadi.

Dan adaidaita ya mayar da kudin tsintuwa

Kara karanta wannan

Dakaru sun kara yin gagarumar nasara, sojoji sun hallaka abokin Bello Turji

A baya mun ruwaito cewa wani dan adaidaita sahu a jihar Kano, Safiyanu Mohammed ya mika wata jakar kudi da ya tsinta a cikin baburinsa daga titin Hadejia a kwanar Dakata.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan Kano, SP Abdullahi Kiyawa ya yi cigiyar mai jakar, tare da neman mai ita ya ziyarci hedikwatar yan sanda a Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.