Yunwa na Neman Kashe Shi a Katsina, Kwankwaso Ya Ceci Ran Karamin Yaro

Yunwa na Neman Kashe Shi a Katsina, Kwankwaso Ya Ceci Ran Karamin Yaro

  • Wani yaro mai shekaru 13, Abubakar Ibrahim ya samu lafiya bayan ya samu taimakon Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso
  • Abubakar Ibrahim, yaro ne 'dan asalin jihar Katsina ne da ke fama da cutar matsananciyar yunwa da ake kira tamowa
  • An kawo yaron asibiti a Kano, kuma ya murmure an mayar da shi gaban iyayen shi a Katsina inda ya ke kara samun sauki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina - Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya kai wa wani yaro mai shekaru 13 taimakon ceton rai a Katsina.

An gano bidiyon yaron mai suna Abubakar Ibrahim ya na yawo a shafukan sada zumunta da yunwa baro-baro a jikinsa.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa Tinubu ya tsawatarwa 'yan siyasa ana saura awanni a yi zaben Edo

Kwankwaso
Sanata Kwankwaso ya dauki nauyin lafiyar yaro mai cutar tamowa Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Jaridar Daily Nigerian ta wallafa cewa yaron mazaunin Yammawa ne a jihar Katsina, kuma tamowa ta masa illar da ake zaton za ta kashe shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso ya tallafa wa yaro 'dan Katsina

Jaridar Pulse Nigeria ta wallafa cewa jagoran jam'iyyar NNPP na kasa, Rabi'u Musa Kwankwaso ya dauki nauyin lafiyar Abubakar Ibrahim.

Shugaban NNPP na jihar Katsina, Armaya'u AbdulKadir ne ya tabbatar da haka, inda ya ce Sanata Kwankwaso ya bayyana shirin daukar nauyin kula da lafiyar yaron.

Yadda Kwankwaso ya dauki nauyin 'dan Katsina

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayar da umarnin mika yaron da ke fama da cutar yunwa a Katsina zuwa asibiti domin samun lafiya.

Tuni aka mika yaron asibitin Abdullahi Wase, da aka fi sani da asibitin Nasarawa a Kano, inda rahotanni su ka bayyana cewa ya murmure har ma an mayar da shi gaban iyayensa.

Kara karanta wannan

Kano: PDP na tsaka da kokarin warware rikicinta, 'yan jam'iyyar sun koma APC

Sanata Kwankwaso ya tallafa wa Borno

A baya mun ruwaito cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Rabi'u Musa Kwankwaso ya kai ziyara Maiduguri, babban birnin jihar Borno inda ya bayar da tallafin N50m.

Ziyarar na zuwa bayan ambliyar da aka wayi garin Talata da ita, inda ruwa ya mamaye akasarin Maiduguri tare da jawo mutuwar sama da mutum 37.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.