An Bukaci a Nemo, a Tono Gawar Sarkin Gobir daga inda Yan Bindiga Suka Birne

An Bukaci a Nemo, a Tono Gawar Sarkin Gobir daga inda Yan Bindiga Suka Birne

  • Kungiyar cigaban Gobirawa a jihar Sokoto ta tura buƙata ga gwamnatin Sokoto da gwamnatin tarayya kan gawar Sarkin Gobir
  • Kakakin kungiyar ya ce suna bukata a samo musu gawar Sarkin domin jama'arsa su masa janaza yadda addini ya tanadar
  • Farfesa Iliyasu Yusuf ya ce Gobirawa ba su ji dadin yadda mai alfarma Sarkin Musulmi ya mu'amalance su ba kan rashin da suka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Ƙungiyar cigaban Gobir (GDA) ta tura buƙata ga gwamnati kan samun gawar marigayi mai martaba sarkin Gobir Alhaji Isa Muhammad Bawa.

Hakan na zuwa ne bayan yan bindiga masu garkuwa da mutane sun kashe sarkin Gobir ba tare da sakin gawarsa ba.

Kara karanta wannan

Wasu dattawa sun sake taɓo batun kisan Sarkin Gobir, sun roki alfarmar Tinubu da gwamna

Gobir
An bukaci samo gawar sarkin Gobir. Hoto: Hadi Muhammad
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa kakakin kungiyar GDA ya ce akwai bukatar ba mutanen Sabon Birni kariya daga yan bindiga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bukatar tono gawar marigayi sarkin Gobir

Kungiyar cigaban Gobir (GDA) ta yi kira ga gwamnatin Sokoto da ta tarayya kan nemo gawar marigayi Alhaji Isa Muhammad Bawa.

Kakakin kungiyar, Farfesa Iliyasu Yusuf Gobir ya ce suna kira ga gwamnati ta yi dukkan mai yiwuwa wajen samo gawar sarkin domin masa janaza cikin mutunci.

Mutanen Gobir sun soki sarkin Musulmi

Kungiyar GDA ta nuna bacin rai a kan cewa ba ta samu kulawa yadda ya kamata daga mai Alfarma Sarkin Musulmi ba.

GDA ta ce fadar mai alfarma Sarkin Musulmi ta gaza tabuka komai tun lokacin da aka kama sarkin da kuma kisan gilla da aka yi masa.

GDA ta bukaci kara tsaro a Sabon Birni

Kara karanta wannan

Ambaliya: Gwamnatin tarayya, Dangote, Dantata da wadanda su ka ba Borno tallafi

Kungiyar GDA ta ce akwai bukatar kara kaimi wajen yakar yan bindiga a Sokoto ta gabas da yankin Sabon Birni.

Punch ta wallafa cewa GDA ta kuma yi kira kan bayar da kulawa ga masu gudun hijira da suke cikin mawuyacin hali a yankuna daban daban.

Matasa sun yi zanga zanga a Gobir

A wani rahoton, kun ji cewa fusatattun matasa sun gudanar da zanga-zanga a garin Sabon Birni na jihar Sokoto kan kisan da ƴan bindiga suka yi wa Sarkin Gobir.

Matasan sun yi ƙone-ƙone a kan tituna bayan sun fusata sakamakon hallaka Alhaji Isa Muhammad Bawa da ƴan bindigan suka yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng