Sarkin Gobir: Jerin Manyan Sarakunan Gargajiya na Najeriya da Suka Rasu a 2024

Sarkin Gobir: Jerin Manyan Sarakunan Gargajiya na Najeriya da Suka Rasu a 2024

A cikin watanni 8 na shekarar 2024, an samu mace-macen manyan sarakunan gargajiya na Najeriya, wadanda da yawansu masu daraja lamba daya ne.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kowanne basarake da abin da ya zama silar ajalinsa, kama daga rashin lafiya ko kuma dai kisan 'yan bindiga, kamar yadda muka gani a mutuwar Sarkin Gobir.

Bayanin sarakunan Najeriya 7 da suka rasu a shekarar 2024
Akalla sarakunan gargajiya 7 ne suka rasu a Najeriya a shekarar 2024. Hoto: @oyostategovt, @KKSY_Reporters, @Imranmuhdz
Asali: Twitter

Domin tunawa da kuma alhinin babban rashin da kasar ta yi na hazikan sarakuna iyayen kasa, mun tattaro manyan sarakuna bakwai da suka rasu a 2024.

1. Sarkin Ningi: Alhaji Yunusa Danyaya

A ranar Lahadi, 25 ga watan agusta ne muka ruwaito cewa Allah ya karbi rayuwar Sarkin Ningi, Mai Martaba, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya fadi basarake 1 da ya nuna damuwa kan halin da ya shiga a 2020

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakataren masarautar Ningi, Alhaji Usman Sule wanda ya sanar da rasuwar ya ce Alhaji Yunusa ya rasu yana da shekaru 80 a duniya.

2. Sarkin Gobir: Alhaji Isa Bawa

Duk da cewa ba a san ainihin ranar da 'yan bindiga suka kashe Sarkin Gobir na Sabon Birni ba, amma labarin mutuwar Alhaji Isa Bawa ta fita ne a ranar Laraba, 21 ga watan Agusta.

An rahoto cewa wasu 'yan bindiga ne suka kashe Sarkin Gobir wata daya bayan da suka yi garkuwa da shi tare da dansa, inda suka sanya kimanin N50m kudin fansarsa.

3. Sarkin Akinale: Oba Olufemi Ogunleye

Sarkin Akinale wanda ake kira da Towulade na Akinale a ƙaramar hukumar Ewekoro, jihar Ogun, Oba Olufemi Ogunleye ya rasu a ranar Laraba, 19 ga watan Yuni.

Fitaccen basaraken mai daraja ya rasu ne yana da shekaru 79 a duniya kuma ya rasu ne a wani asibitin Landan inda ya ke jinyar rashin lafiyarsa.

Kara karanta wannan

Magani na gagarar talaka: Masu ciwon sukari sun nemi alfarma wajen Shugaba Tinubu

4. Sarkin Tikau: Alhaji Muhammadu Abubakar

Alhaji Muhammadu Abubakar Ibn Grema, Sarkin masarautar Tikau da ke jihar Yobe ya rasu a ranar Juma'a, 10 ga watan Mayun 2024.

Basaraken, wanda ya koma ga mahaliccinsa yana da shekaru 74, an ce ya rasu ne a asibitin kwararru da ke garin Potiskum bayan ya sha fama da rashin lafiya.

5. Sarkin Idanre: Oba Frederick Aroloye

Allah ya karbi rayuwar sarki mai daraja ta daya a jihar Ondo, Owa na masarautar Idanre, Oba Frederick Adegunle Aroloye a safiyar Laraba, 31 ga watan Yulin 2024.

An rahoto cewa Oba Aroloye (Arubiefin na IV) ya rasu ne yana da shekaru 102 a duniya, kamar yadda Cif Christopher Oluwole Akindolire ya sanar.

6. Sarkin Asagba: Joseph Chike Edozien

Mun rahoto cewa Mai martaba Obi (Farfesa) Joseph Chike Edozien, sarkin masarautar Asagba na 13 ya rigamu gidan gaskiya yana tsaka da shirin cika shekaru 100 a duniya.

Kara karanta wannan

Nuhu Ribaɗu ya yi babban rashi, Allah ya yiwa surukarsa rasuwa a Abuja

Sarkin wanda ya rasu a ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairun 2024 an ce mutuwarsa ta girgiza mutanen yankin Delta wadanda suke kallonsu a matsayin babban uba.

7. Sarkin Ibadan: Oba Lekan Balogun

Sarkin kasar Ibadan na 42 a tarihi, Oba Lekan Balogun ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 82 a duniya, kuma ya shafe shekaru 2 ne kacal a kan karagar mulkin.

Gwamnatin jihar Oyo wadda ta fitar da sanarwar rasuwar basaraken ta ce Oba Balogun ya rasu a asibitin jami'a na UCH ranar Alhamis, 14 ga watan Maris, 2024.

Uwar gidan Sarki Shehu ta rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa allah ya karbi rayuwar Hajiya Habiba Shehu Idris, uwa gidan tsohon sarkin Zazzau, marigayi Alhaji Shehu Idris.

Masarautar Zazzau ta fitar da sanarwar cewa Hajiya Habiba ta rasu ne a safiyar Juma'a, 30 ga watan Agustan 2024 bayan fama da 'yar gajeruwar jinya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.