Kwara: Ana cikin Halin Kunci, Dattijuwa Mai Shekara 54 Ta Haifi Jarirai 11, Miji Ya Kidime

Kwara: Ana cikin Halin Kunci, Dattijuwa Mai Shekara 54 Ta Haifi Jarirai 11, Miji Ya Kidime

  • Abin mamaki ya afku bayan wata mata mai shekaru 54 ta haifi jarirai 11 a kasar Jamhuriyar Benin da ke makwabtaka da Najeriya
  • Matar wacce ita da mijinta yan asalin jihar Kwara ne sun bukaci taimakon al'umma ta kowane bangare saboda halin da suke ciki
  • Mijin matar mai suna Nafi'u Yahaya ya roki al'umma taimako musamman na kudi inda ya ce iyalansa suna cikin wani hali a yanzu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kwara - Wani magidanci mai shekaru 56 a jihar Kwara ya shiga damuwa bayan matarsa ta haifi jarirai 11.

Magidancin mai suna Yahaya Nafi'u da ke birnin Ilorin ya bukaci al'umma su taimaka masa saboda halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Fada ya barke tsakanin makiyaya da manoma a Arewacin Najeriya, an kashe mutum

Mata ta haifi jariarai 11 bayan shafe shekaru 3 da juna biyu
Wata mata mai dauke da juna biyu na tsawon shekaru 3 ta haifi jarirai 11. Hoto: Voice of Nigeria.
Asali: UGC

Kwara: Dattijuwa ta haifi jarirai 11

Matar mai shekaru 54 da ake kira Alake ta haifi jariran ne a Cotonou da ke Jamhuriyar Benin, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nafi'u ya tabbatar da cewa jarirai mata guda biyu sun rasu yayin ya rage saura maza takwas da mace daya.

Ya ce sauran jariran guda tara suna cikin koshin lafiya inda ya koka cewa yana cikin mawuyacin hali, Premium Times ta tattaro.

Rahotannin sun tabbatar da cewa an haifi wasu daga cikin jariran a ranar 7 ga watan Yulin 2024, sai sauran kuma a ranar 14 ga watan Yuli.

Yadda mutuniyar Kwara ta haifi jarirai 11

"Kwanaki kadan bayan haifar wasu jariran, mahaifiyarsu ta ce tana jin wani irin abu a cikinta."
"Bayan zuwa asibiti sai aka dauki hoto inda likita ya tabbatar da cewa akwai sauran wasu jarirai."

Kara karanta wannan

Rikici na neman ruguza APC a jihar Arewa, jam'iyya ta kira taron gaggawa

- Yahaya Nafi'u

Uwa da 'ya 'yanta sun rasu a Kwara

Kun ji cewa mutum huɗu ƴan gida ɗaya da suka haɗa da uwa da yara uku sun mutu bayan sun ci shinkafa a Ilọrin babban birnin jihar Kwara.

Lamarin ya faru ne a unguwar Oshin da ke kan titin Asa Dam a ranar Asabar da ta gabata, 17 ga watan Agusta, 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.