Kekere Ekun: Abubuwa 4 da Muka Sani game da sabuwar Shugabar Alkalan Najeriya

Kekere Ekun: Abubuwa 4 da Muka Sani game da sabuwar Shugabar Alkalan Najeriya

Abuja - Yayin da ake sa ran samun gagarumin sauyi a fannin shari’ar Najeriya, kallo ya koma kan Mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun, wacce ana rantsar matsayin shugabar alkalan kasar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A yau Juma'a, 23 ga watan Agusta ne Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da Kudirat Kekere-Ekun domin ta gaji Mai shari'a Olukayode Ariwoola wanda ya yi ritaya ranar Alhamis.

Abubuwa 4 da ya kamata ku sani game da Kudirat Kekere-Ekun, sabuwar shugabar alkalan Najeriya.
Abubuwa 4 da ya kamata ku sani game da sabuwar shugabar alkalan Najeriya. Hoto: @ataweweattorney
Asali: Twitter

A wani rahoto da jaridar The Nation ta wallafa, mun tattaro wasu muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da sabuwar shugabar alkalan Najeriya.

Abubuwa 4 game da Kekere-Ekun

1. Samun daukaka a aikin shari'a

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya rantsar da sabuwar shugabar alkalan Najeriya, bayanai sun fito

Mai shari’a Kekere-Ekun ta yi fice a fannin shari’a, inda ta fara zama alkaliyar babbar kotun jihar Legas a shekarar 1996.

Kara mata matsayi zuwa Kotun Daukaka Kara a shekara ta 2004 ya fito da kwarewarta a jagorantar sassa biyar na kotun.

Ta kai ga kololuwar aikinta ne a lokacin da aka nada ta a matsayin mai shari’a a Kotun Koli a watan Yulin 2013, inda ta ci gaba da bayar da gudunmawa sosai a fannin shari’a a Najeriya.

2. Ilimi mai zurfi kan shari'a

Wanda aka haifa a Landan a ranar 7 ga Mayu, 1958, Mai shari’a Kekere-Ekun ta halarci kwalejin sarauniya da ke Legas, sannan ta karanci shari’a a jami’ar Legas (UNILAG) daga 1977 zuwa 1980.

Neman karatun ta bai tsaya nan ba; ta samu digiri na biyu a fannin shari'a daga babbar makarantar London ta (LSE) a 1983, wanda ya ta kara tabbatar da kafuwarta a ilimi.

Kara karanta wannan

Tinubu ya dawo Najeriya daga Faransa, zai rantsar da sabuwar shugabar alkalai

3. Ajiye tarihi a aikin gwamnati

Mai shari’a Kekere-Ekun ta fito ne daga dangi da ke da tarihin hidimar aikin gwamnati, ita ce babba ga a cikin 'ya'ya 11.

Mahaifinta, Marigayi Sanata H.A.B Fasinro, mutum ne mai sadaukarwa ga iyalansa a Legas, yayin da mahaifiyarta, Misis Winifred Ogundimu (née Savage), ta yi fice a aikin gwamnati.

Babu shakka wannan tarihi na aikin gwamnati a zuriyarta ya yi tasiri a kan jajircewar Kekere-Ekun wajen yiwa Nijeriya hidima ta fuskar shari’a.

4. Jagora a garambawul din shari'a

A tsawon rayuwarta, Mai shari’a Kekere-Ekun ta kasance kan gaba wajen kawo sauyi a harkokin shari’a a Najeriya.

Ta kasance Mai shari'a ta farko kotun daukaka kara ta reshen Makurdi, sannan ta zama shugabar alkalan kotun ta reshen Akure.

Jagorancinta ya wuce harabar kotu saboda ita 'yar kwamitin shari'a na kotun koli ce kuma tana jagorantar kwamitin kulawa na sashen shari'a na kotun.

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya kammala digirin digirgir, ya samu PhD da rigimar sarauta ta lafa

NJC ta gabatar da Kekere-Ekun

Tun da fari, mun ruwaito cewa majalisar shari'a ta Najeriya (NJC) ce ta gabatar da sunan Mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun ga shugaba Bola Tinubu domin a yi mata nadin babbar alkali.

Majalisar ta nuna cewa Mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun ta mallaki dukkanin abubuwan da ake bukata ta zama shugabar alkalan kasar bayan ritayar Olukayode Ariwoola.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.