An yi Jana'izar Sarki Gobir a Fadarsa cikin Yanayin Jimami

An yi Jana'izar Sarki Gobir a Fadarsa cikin Yanayin Jimami

  • Al'umma da dama a Sokoto sun halarci sallar janazar da aka yiwa sarkin Gobir, Alhaji Isa Muhammad Bawa a yau Alhamis
  • An yi janazar sarkin ne irin yadda ake sallar wanda ba a samu gawarsa ba bayan mutuwa kamar yadda addinin Musulunci ya koyar
  • A ranar Laraba ne yan bindiga masu garkuwa da mutane suka kashe sarkin bayan ya shafe sama da makonni uku a wajensu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Al'ummar Musulmi a jihar Sokoto sun halarci sallar gawar da aka shirya wa marigayi sarkin Gobir, Alhaji Isa Muhammad Bawa.

Marigayin ya rasu ne a hannun yan bindiga da suka kashe shi bayan sun yi garkuwa da shi yana tafiya fadarsa daga Sokoto.

Kara karanta wannan

'An zalunci yan bindiga,' Sheikh Gumi ya yi magana bayan kisan sarkin Gobir

Sarkin Gobir
An yi janazar sarkin Gobir. Hoto: Mudassir Ibrahim Mando Kaduna
Asali: Facebook

Rahoton BBC Hausa ya nuna cewa a yau Alhamis al'umma suka yi janazar marigayi Alhaji Isa Muhammad Bawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan bindiga sun hana gawar sarkin Gobir

Legit ta ruwaito cewa bayan an biya kudin fansa da yan bindiga suka bukata sun hana gawar sarkin Gobir.

Yan bindigar sun bayyana cewa sun riga sun birne sarkin bayan sun kashe shi amma sun sake dan shi mai suna Kabiru Isa.

Yadda aka yi janazar sarkin Gobir

Al'ummar Musulmi sun taru wajen gudanar da janazar sarkin Gobir kasancewar ba a samu gawarsa ba.

Dama addinin Musulunci ya tanadi tsari wajen yin sallar janaza idan aka rasa gawar wanda ya mutu kuma haka aka yiwa sarkin.

A ina aka yi jana'izar sarkin Gobir?

Rahotanni sun nuna cewa an yi janazar marigayi Alhaji Isa Muhammad Bawa ne a fadarsa da ke Sabon Birni.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi martani mai zafi kan mutuwar Sarkin Gobir, ya fadi laifin gwamnatin Tinubu

Daruruwan mutane ne daga wurare daban-daban suka halarci sallar janazar cikin yanayi na nuna alhini.

Yan bindiga sun sace mutane a Kaduna

A wani rahoton, kun ji cewa yan bindiga ɗauke da makamai sun kai farmaki a ƙauyen Galadimawa da ke ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Rahotanni na nuni da cewa miyagun ƴan bindigan sun yi awon gaba da matar basaraken ƙauyen tare da ƴaƴansa guda biyu a yayin harin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng