Sarki Sanusi II na Shirin Zama Dakta, babu Kuskure a Kundin Binciken da Ya Rubuta

Sarki Sanusi II na Shirin Zama Dakta, babu Kuskure a Kundin Binciken da Ya Rubuta

  • Jami'ar SOAS da ke kasar Ingila ta yi wa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II albishir da kammala karatunsa na digirin digirgir
  • Wakilan jami'ar da suka tattauna da Sarki Sanusi II sun shaida masa cewa ba su samu wani kuskure a takardar binciken da ya yi ba
  • Jin cewa babu gyara a bincikensa, an ga Sarki Sanusi II a cikin bidiyo yana nuna murnarsa a fili, yayin da ya ke shirin zama Dakta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya cika da tsananin farin ciki a lokacin da jami'ar SOAS ta Ingila ta sanar da shi cewa babu gyara a binciken da ya yi.

Sarki Sanusi II ya gudanar da bincike kan amfani da dokokin iyali na addinin musulunci wajen daidaita rayuwar jama'a, a wani mataki na kammala digirin digirgir.

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya kammala digirin digirgir, ya samu PhD da rigimar sarauta ta lafa

Jami'ar SOAS da ke Ingila ta yiwa Sarki Sanusi II albishir da zama Dakta
Sarki Sanusi II zai zama Dakta bayan jami'ar Ingila ta amince da bincikensa. Hoto: @masarautarkano
Asali: Twitter

A cikin wani faifan bidiyo da shafin masarautar Kano ya wallafa a kafar X, an ga Sarki Sanusi II zaune gaban na'ura mai kwakwalwa yana tattaunawa da malamansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babu kuskure a binciken Sarki Sanusi II

A cikin bidiyon, an ji wani daga cikin wakilan jami'ar na cewa:

"Ina taya ka murna, musamman kasancewar ni ne wanda zan fara taya Sarki Sanusi murna na tsallake wannan jarabawa ba tare da an ci shi wani gyara ba.
"Takardar binciken da ya rubuta ta samu karbuwa, kuma an tabbatar da ita bisa yardar alkalai biyu da suka duba binciken bayan an gabatar da shi."

Muhammadu Sanusi II zai zama Dakta

Mai maganar ya ci gaba da cewa:

"Babu wani sauran aiki da za a yi kan wannan takardar bincike, kuma dama wannan nan daga cikin abubuwan da ake bukata a matakin samun PhD.

Kara karanta wannan

Bacin ciki: Jihohin Najeriya 6 da mutane 43 suka rasa rayukansu daga cin abinci

"Don haka ina taya ka murna, zan iya cewa Dakta Sanusi, duk da cewa ba wai an tabbatar da hakan ba ne, amma dai dukkanin matakai sun kammala."

Kalli murnar da sarkin ya yi a cikin wannan bidiyo a kasa:

Sarki Sanusi II ya kammala digirin digirgir

Tun da fari, mun ruwaito cewa mai martaba Muhammadu Sunusi II ya kammala karatunsa a fannin shari'ar addinin musulunci a jami'ar SOAS.

An ruwaito cewa Sarkin Kano Sunusi II ya fara karatun ne a Ingila bayan gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta tsige shi daga karagarsa a 2020.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.