Sanusi ya bukaci gwamnati ta kayyadewa 'yan Najeriya yawan iyalin da za su haifa
- Tubabben sarkin Kano, Sanusi II ya bukaci gwamnati da ta saka dokar kayyade yawan iyali
- Tsohon shugaban babban bankin ya ce hakan ne kawai zai kawo daidaituwar yawan 'yan Najeriya
- Muhammadu Sanusi ya ce ba Musulunci bane haifar yaran da ba za a iya kula da su da kyau ba
Tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi II yayi kira ga gwamnati da ta saka tsauraran dokoki da za su daidaita hauhawar yawan jama'a a kasar nan.
Sanusi wanda yayi magana a ranar Laraba yayin wani taro a Legas, ya ce ya dace jama'a su dinga haifar yaran da za su iya kula da su, Daily Trust ta wallafa.
Kamar yadda tsohon gwamnan babban bankin Najeriya yace, abubuwan da ke bayyana a halin yanzu sun nuna cewa gwamnati ba za ta iya samar da dukkan ababen more rayuwa da ake bukata ba.
KU KARANTA: Da duminsa: COAS na Goodluck Jonathan ya sauya sheka, ya koma jam'iyyar APC
Sanusi ya kushe yadda ake haihuwa a kasar nan ba tare da karfin kula da yaran ba, wanda yace hakan ba daidai bane ko a addinin Musulunci.
Ya ce: "Yadda jama'a ke auren duk yawan matan da suke so ba tare da wata dokar da ta gindaya yawan yaran da za a haifa ba bai dace ba ko a Musulunci.
"Ban san dalili ba amma akwai doka a Musulunci da ta hana tara iyali ba tare da kayyade su ba. Babu wani tabbacin cewa za a iya kula dasu ba tare da an yi watsi da dawainiyarsu ba."
KU KARANTA: Yara 7 sun samu rauni bayan 'abu mai fashewa' ya tarwatse suna wasa dashi a Kaduna
A wani labari na daban, tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba zai samu damar tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar APC ba a zaben shugaban kasa 2023.
Saraki ya bayyana hakan a ranar Talata bayan ya tasa 'yan kwamitin sasanci na jam'iyyar PDP zuwa gidan tsohon shugaban kasar dake Abuja.
A taron da suka yi da Jonathan an samu labarai iri-iri na batun shugabannin jam'iyyar APC da tsohon shugaban kasar wanda ya janyo cece-kuce iri-iri a kafafen sada zumuntar zamani, inda har wasu suke zaton APC za ta tsayar da Jonathan takara a 2023.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng