Abubuwa 6 da ya Kamata Ku Sani kan Marigayi Sarkin Gobir da Masarautarsa

Abubuwa 6 da ya Kamata Ku Sani kan Marigayi Sarkin Gobir da Masarautarsa

  • A yau Laraba aka wuni da labarin kisan mai martaba sarkin Gobir, Alhaji Isa Muhammad Bawa a hannun yan bindiga a jihar Sokoto
  • Sarkin Gobir ya shafe kimanin makonni uku a hannun yan bindiga inda miyagun suka buƙaci kudin fansa ko kuma su kashe shi har lahira
  • A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku wasu muhimman abubuwa da suka shafi rayuwar sarkin Gobir, Alhaji Isa Bawa da masarautarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Rahotanni sun tabbatar da cewa yan bindiga da suka yi garkuwa da sarkin Gobir, Alhaji Isa Muhammad Bawa sun kashe shi.

Kafin kisan sarkin, ya fito ya nemi taimako daga al'umma da gwamnatin Sokoto domin a kubutar da shi.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun harbe sarkin Gobir, sun rike dansa a jeji

Sarkin Gobir
Muhimman abubuwa kan sarkin Gobir. Hoto: Hadi Muhammad
Asali: Facebook

A wannan rahoton mun tattaro muku wasu muhimman abubuwa da suka shafi sarkin Gobir da masarautarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muhimman abubuwa kan Sarkin Gobir

  1. Sarkin Gobir, Alhaji Isa Muhammad Bawa ya rasu yana da shekaru 74 da haihuwa kamar yadda ya bayyana da bakinsa a bidiyon da aka masa.
  2. Alhaji Isa Muhammad Bawa ya bayyana cewa ya shafe shekaru 45 yana harkar sarauta inda ya rike matsayi daban daban.
  3. Rahoton DW ya nuna cewa yan bindiga sun bukaci a ba su kudin fansa har N60m tare da babura biyar.
  4. Vanguard ta wallafa cewa a watan Afrilu da ya wuce gwamnatin Sokoto ta rage darajar Sarkin Gobir, Alhaji Isa Bawa inda aka dauke shi daga sarautar Sabon Birni zuwa Gatawa.
  5. RFI Hausa ta bayyana cewa masarautar Gobir ta kafu ne tun kafin zuwan Shehu Usmanu Danfodiyo kasar Hausa. Ana hasashen cewa masarautar ta kafu ne a karni na 11.
  6. Tarihin baka ya nuna cewa Gobirawa suna iƙirarin cewa asalinsu daga kasar Saudiyya suka taso a wani gari mai suna Gubari.

Kara karanta wannan

Mutumin Jonathan ya tono makircin da ake shiryawa Tinubu a Arewa bayan sayen jirgin sama

An kama masu safarar makamai

A wani rahoton, kun ji cewa jami’an sashen yaki da masu garkuwa da mutane na rundunar ‘yan sandan Kaduna sun cafke masu safarar makamai ga ‘yan bindiga.

Wadanda ake zargin da suka amsa laifinsu, Abdulaziz Habibu da Nuhu Thomas mazauna Dogon Dawa ne da ke a Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng