An Yi Mutuwar da Ta Kaɗa Bola Tinubu, Shugaban Kasa Ya Tura Sakon Ta’aziyya

An Yi Mutuwar da Ta Kaɗa Bola Tinubu, Shugaban Kasa Ya Tura Sakon Ta’aziyya

  • Shugaba kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna damuwa kan mutuwar tsohon shugaban harkokin wasanni a Afrika (CAF)
  • Rahotanni sun nuna cewa tsohon shugaban CAF, Issa Hayatou ya rasu ne a yammacin jiya Alhamis yana mai shekaru 77 a duniya
  • Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya ce rashi ne babba ga al'ummar yankin Afrika ba kawai ga iyalan marigayi Issa Hayatou ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya nuna damuwa kan mutuwar tsohon shugaban CAF, Issa Hayatou.

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya ce marigayin ya bayar da gudummawa sosai ga harkar wasanni a yankin Afrika.

Kara karanta wannan

Shugaban APC ya fadawa Tinubu hanyar da zai shirya da talakawa bayan zanga zanga

Shugaba Tinubu
Tinubu ya nuna damuwa kan rasuwar Issa Hayatou. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa a yau Jumu'a ne Bola Ahmed Tinubu ya tura saƙon ta'aziyya ga iyalan marigayin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe Issa Hayatou ya rasu?

Rahotanni sun nuna cewa a jiya Alhamis ne tsohon shugaban CAF, Issa Hayatou ya rasu yana da shekaru 77 a duniya.

Marigayin ya kasance jagora a harkar wasanni a yankin Afrika kuma ya taba zama mukaddashin shugaban hukumar wasanni ta duniya, FIFA.

Tinubu ya yi ta'aziyyar Issa Hayatou

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tura sakon ta'aziyya ga dukkan yan kasar Kamaru da masu harkar wasanni a Afrika.

Rahoton Channels Television ya nuna cewa Bola Tinubu ya ce rasuwar Issa Hayatou babbar asara ce ga duniyar wasanni.

Gudummawar Issa Hayatou ga wasanni

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce Issa Hayatou ya ba da gudunmawa sosai a harkar wasanni a Afrika da faɗin duniya.

Kara karanta wannan

An yi rashi a duniyar kwallon kafa, tsohon shugaban hukumar CAF, Issa Hayatou ya rasu

A ƙarshe, shugaba Bola Tinubu ya yi addu'ar samun rahama ga marigayi Issa Hayatou da tura sakon karfafawa ga dukkan iyalansa.

Rasuwar sarki: Tinubu ya tura sakon ta'aziyya

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa ya tura sakon jaje bayan mutuwar sarkin da ya fi daɗewa a kan karaga a Arewacin Najeriya.

Bola Tinubu ya ce yana yiwa dukkan mutanen masarautar Asholyio da ma daukacin al'ummar kudancin Kaduna jaje kan babban rashin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng