"Ina Asusun Bankinku": Bidiyon Yadda Tsofaffi Mata Ka Aikin Leburanci, an So Taimakonsu
- Mutane da dama sun shiga wani irin yanayi bayan ganin wani faifan bidiyo na wasu tsofaffi mata suna aikin leburanci
- A cikin faifan bidiyo an gano tsofaffin guda biyu suna daukar kwangiri a kansu cike da kwababben siminti da kasa
- Mutane da dama sun yi martani inda wasu ke ganin jarumtakarsu yayin da wasu ke tausaya musu ganin yadda suka tsufa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Wani faifan biyidon ta tayar da hankalin jama'a bayan ganin wasu dattijai mata biyu na aikin leburanci.
An gano matan na daukar kwangiri cike da kasa da kwababbiyar siminti suna kai wa domin gini.
Yadda tsofaffi mata ke aikin leburanci
A wani faifan bidiyon Tiktok wanda @adeijebi ta wallafa an gano tsofafifn ana zuwa musu siminti a kwangiri suna kai wa inda ake gini.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan cika musu kwangiri da kwababben siminti, tsofaffin za su dauka a kansu domin kai wa inda ake bukata a wurin da ake gini.
An yi ta yaɗa faifan bidiyon a kafafen sada zumunta inda mutane da dama suka yi martani tare da nuna tausayinsu a fili.
Mutane da dama sun yaba da kokarin tsofaffin inda wasu kuma suke tausaya musu ganin yawan shekarunsu.
Martanin mutane bayan kallon faifan biyidon:
@pretty_Blessing:
"Don Allah ku yi mata bidiyo yadda za ta fadi lambar asusun bankinta."
@BigStar:
"Kai, wannan abin ya taba min zuciya ta matuka, Allah ka taimake ni na taimakawa wasu."
@NkemDavid:
"Gwara na sayar da hanta na da na ga mahaifiyata ta na wannan aiki."
Bidiyon dogon matashi dan aji 4 a firamare
Kun ji cewa an yaɗa bidiyon wani yaro wanda har yanzu ba a bayyana shekarunsa ba ya dauki hankali matuka saboda matukar tsayi da ya ke da shi.
Tuni masu amfani da shafukan sada zumunta su ka yi ta magantuwa kan irin baiwar tsayin yaron, yayin da wasu ke ganin abin da mamaki.
Duk da ba a fadi takaimaimai garin da yaron ya fito ba, an bayyana cewa dan kasar Sudan ta Kudu ne da ke Afrika ta Gabas.
Asali: Legit.ng