Tuna Baya: Shehu Sani Ya Bayyana Yadda Ya Ceto Obasanjo Daga Shan Duka a Gidan Yari

Tuna Baya: Shehu Sani Ya Bayyana Yadda Ya Ceto Obasanjo Daga Shan Duka a Gidan Yari

  • Sanata Shehu Sani ya bayyana yadda suka yi zaman gidan yari cikin tsanani tare da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo
  • Shehu Sani ya bayyana yadda manyan barayi suka nufi yiwa tsohon shugaban kasar duka a gidan yarin amma ya ba shi kariya
  • Cif Olusegun Obasanjo da Shehu Sani sun yi zaman gidan yari ne a karkashin mulkin soja na Janar Sani Abacha a shekarar 1995

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Sanata Shehu Sani ya bayyana yadda suka yi fama a gidan yari tare da tsohon shugaban kasa cif Olusegun Obasanjo.

Shehu Sani ya fadi yadda wanda aka haɗa daki dasu suka yi yunkurin yiwa tsohon shugaban ƙasar duka.

Kara karanta wannan

2027: Shehu Sani ya bayyana matakin da 'yan siyasar Arewa suka dauka domin kayar da Tinubu

Shehu Sani
Yadda Shehu Sani ya ceci Obasanjo daga shan duka. Hoto: Senator Shehu Sani, Gabriel Aponte
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Sanata Shehu Sani da Cif Olusegun Obasanjo sun yi zaman yari ne a lokacin mulkin Janar Sani Abacha.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin kama Shehu Sani da Obasanjo

A lokacin mulkin Janar Sani Abacha a shekarar 1995 aka kama Shehu Sani saboda adawa da mulkin soja.

Haka zalika a lokacin aka kama Olusegun Obasanjo bisa zargin kitsa juyin mulki ga gwamnatin Janar Sani Abacha.

An daure Shehu Sani da Obasanjo

Biyo bayan kama Shehu Sani da Obasanjo ne aka mikasu gidan yarin Kirikiri domin cin sarka, rahoton the Cable.

Shehu Sani ya bayyana cewa a lokacin an yanke musu zaman gidan kaso na shekaru 15 saboda laifuffukan da aka zargesu da aikatawa.

Yadda aka so yiwa Obasanjo duka

Sanata Shehu Sani ya labarta cewa ana isa da su kurkuku sai barayin da suke ɗaƙi daya suka fara zagi da hantarar Obasanjo.

Kara karanta wannan

Gwamnan Zamfara na shan sukar gina filin jirgin saman N62.8b ana fama da 'yan bindiga

Ana cikin haka ne sai Shehu Sani ya ce musu shi ne jagora a dakin, su dakata, ya kuma fadawa ɓarayin cewa yanzu Obasanjo ya dawo dan uwansu a gidan yari.

Saboda haka ne sai suka ɗagawa Olusegun Obasanjo kafa ya samu sauƙin zama a gidan yarin har zuwa lokacin fitarsa.

Yan siyasa sun ziyarci Buhari

A wani rahoton, kun ji cewa manyan yan siyasar Arewa sun yi tururuwa zuwa Daura wajen tsohon shugaban kasa da Muhammadu Buhari.

Cikin manyan yan siyasa da suka je wajensa akwai babban dan jam'iyyar adawa, Atiku Abubakar da jigo a APC, Nasir Ahmed El-Rufai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel