Muhimman Abubuwa 3 da Ya Dace a Sani a Kan Jami’in Kwastam da Ya Mutu a Majalisa

Muhimman Abubuwa 3 da Ya Dace a Sani a Kan Jami’in Kwastam da Ya Mutu a Majalisa

  • A yau Talata ne babban jami'in kwastam mai suna, Etop Andrew Essien ya fadi ya mutu yana cikin bayani a majalisar wakilai
  • Hukumar kwastam ta kasa ta fitar da sakon ta'aziyya inda ta ce Etop Andrew Essien jajircaccen jami'in ne da ya yi aiki tukuru
  • A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku abubuwa uku masu muhimmanci da ya kamata ku sani a kan Etop Andrew Essien

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A yau Litinin ne jami'in hukumar kwastam Etop Andrew Essien ya yanki jiki ya fadi yana tsaka da bayani a majalisar wakilai.

Hukumar kwastam ta tabbatar da rasuwarsa tare da tura sakon ta'aziyya ga iyalansa da Najeriya baki daya.

Kara karanta wannan

Mutuwar jami’in Kwastam: Shugaba Tinubu ya aikawa Iiyalin Marigayi Etop Essien saƙo

Hukumar kwastam
Abubuwa masu muhimmanci kan jami'in kwastam da ya mutu a majalisa. Hoto: Uche Nnadozie|House of Representatives, Federal Republic of Nigeria
Asali: Facebook

Legit tattaro muku abubuwa masu muhimmanci a kan Etop Andrew Essien kamar yadda hukumar kwastam ta wallafa a shafinta na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Etop ya shafe shekaru kusan 40 a kwastam

Hukumar kwastam ta tabbatar da cewa Etop Andrew Essien ya shafe shekaru sama da 30 yana aiki tare da ita.

Etop Andrew ya shiga aikin kwastam ne a ranar 27 ga watan Nuwambar shekarar 1989 wanda lissafi ya nuna ya shafe shekaru 35 yana aiki.

2. Etop ya fito daga jihar Akwa Ibom

Bincike ya tabbatar da cewa an haifi Etop Andrew Essien a ranar 16 da watan Nuwamba a shekarar 1967 a jihar Akwa Ibom.

Etop Andrew ya fito ne daga karamar hukumar Nsit-Ubium dake jihar Akwa Ibom a kudu maso kudun tarayyar Najeriya, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Babban jami'in hukumar Kwastam ya mutu ana tsakiyar zaman kwamitin Majalisa

3. Etop ya rike matsayin tattara harajin kwastam

Daga cikin manyan matsayin da Etop Andrew Essien ya rike a hukumar kwastam akwai mataimakin kwanturola a kan harkar tatttara haraji.

A kan wannan matsayin ne kuma Etop ya rigamu gidan gaskiya yayin da yake bayani a majalisar wakilai a yau Litinin, 25 ga watan Yuni.

Kwastam na shirin kawo saukin abinci

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar kwastam ta kasa ta yi alwashin kawo karshen matsalar boye abinci da ta addabi daukacin al'umma.

Kwastam ta ce a yanzu haka ta dauki masu matakai wanda za su kawo karshen matsalar domin kawo saukin rayuwa ga talakawan Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng