Amfani 7 na ganyen Zogale ga jikin mutum

Amfani 7 na ganyen Zogale ga jikin mutum

– Ganyen zogale watau Moringa yana daga cikin ganye masu amfani a Duniya

– Zogale na maganin cututtuka da dama na Dan Adam

– Kadan daga ciki akwai maganin cutar zuciya da kwakwalwa

Amfani 7 na ganyen Zogale ga jikin mutum
Ganyen Zogale na da amfani a jikin mutum

Kusan komai a Zogale yana da amfanin gaske daga itacen, ganyen har tushen. Zogale na maganin cututtuka da dama idan aka yawaita amfani da shi a kai-a kai. Kadan daga ciki:

1. Arthritis

Zogale na maganin wannan mugun cuta mai hana motsi ko tafiya da kyau

2. Cututtukan zuciya

Zogale na maganin cututtukan zuciya inda yake rage kwalasturol din da ke jikin mutum.

3. Gyara kwakwalwa

Zogale na dauke da bitamin irin su E da C da suke taimakawa wajen gyara kwakwalwa su kuma kare cututtuka.

KU KARANTA: Amfanin lemu ga kananan yara

Amfani 7 na ganyen Zogale ga jikin mutum
Ganyen Zogale na da matukar amfani

4. Maganin cutar hunta

Akwai sinadarai da dama a jikin fure da ganyen Zogale sa gyara kare hanta.

5. Ciwon sukari

Zogale na maganin cutar nan ta Diabetes ta hanyar rage yawan sukarin jikin mutum. idan har ana daka ganyen ana sha.

6. Sauran cututtuka numfashi

Zogale na kare mutum daga cututtuka da ke hana numfashi da kyau idan aka sa mu kumburi a huhu.

7. Gyara fata

Haka kuma Zogale na dauke da sinadarai da ke gyara fatar jikin mutum

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Farashin kayan abinci a Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel